Son Imam Aliyu Bn Abi Talib (As) Alamin Imani ne



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Tare da wakilin mu Bin Haroun Sigau

Hakan kuwa ya kan fito fili in muka yi dubi kan hadisan da
suka zo kan son Amirul Muminin (a.s) a matsayin alamar son Ahlulbaiti (a.s).

An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa: "Babu wanda zai yi imani face sai ya so Ahlulbaitina. Sai Umar bn Khattab yace: Menene alamar son Ahlulbaitin naka?
Sai yace:"Wannan" wato yana mai nuni ga Ali (a.s)

Don haka daga nan zamu iya fahimtar cewa ta'akidi
kan son Amirul Muminina (a.s), ta'akidi ne kan son Ahlulbaiti gaba dayan su da kuma riko dasu da kuma koyi da karantar war su.

Saika so su, imanin ka zai zam ya cika, domin ta hanyar sonsu ne kake damfaruwa da ayyuka irin nasu.

Ko waye, dummin ganin girman da kake, ko sunan Sheikh wane ko mai tunjumemen rawani wane, matuƙar ka bincika ka gane makiyi ne ga Imam Ali (As), ti wallahi baida imani, Musluncin sa bai kammala ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post