Shugaban ma'aikata a fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari ya kamu da coronavirus kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa.
Har wa yau, wata majiya mai tushe a fadar gwamnatin ta Najeriya, ta tabbatar wa da BBC labarin cewa " da gaske ne batun Abba kyari ya kamu da coronavirus."
Kafin nan dai BBC ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu kan al'amarin amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.
Reuters dai ta rawaito cewa Abba Kyari ya yi bulaguro zuwa Jamus a farkon watan Maris tare da wata tawagar jami'an gwamnatin kasar domin yin wani taro da kamfanin Siemens.
Sai dai kamfanin na Reuters din ya ce babu tabbas ko Abba Kyari ya killace kansa ko a'a.
Tare da --Idishia Jos.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya