Shekaru hudu, a wane hali jagora yake???



Ma'asumah Nigerian News Update

Rbtw: Suhaila Aminu Sidi

1- Cewa akayi kawai ku rufe kasuwanni da masallatai amma kuna tsuwwa...shikam jagora fiye da shekara hudu an kebanceshi daga mutane.

2- Cewa akayi kusa abun kariya a hancinku (na wani dan lokaci). saboda kar cuta ta kamaku...amma shi cutarce a cikin jikinshi shiyasa yake sanyawa.

3- Cewa akayi ku koma gidajenku ku zauna...amma jagora gidan nashi aka rusa.

4- Ance ku koma cikin iyalanku da 'yan uwanku ku zauna...amma shi jagora 'ya'yan nashi aka kashe aka qona.

5- In kaceman ai talakawa basu da abincin da zasu ci idan suka koma gida...sai ince shi jagora guba ake sanyawa a abincinshi kafin a kawo mashi.

6- Don saboda kar lafiyarka ta cutu aka kulle ka... Amma jagora saboda karya samu lafiya aka kulleshi aka hana likitoci su duba shi (dukda kasancewar harsashe a cikin jikinshi).

★A yanzu ya kamata talaka yayi nazari domin ya gane girman zaluncin da akayiwa bawan Allan nan, sannan yayi mamakin tayaya akayi ya iya kawowa yanzu a raye.

★A yanzu dan uwa ya kamata ya fahimci girman sakacin dayayi game da lafiyar jagoransa, sannan ya tambayi kansa : Shin wane qoqari nayi ko kuma nakeyi domin samun 'yancin sa?.

#FreeZakzaky
#FreeUmmaZeenat.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post