Sheikh Turi A Wajen Malam Zakzaky (H).

Sheikh Zakzaky (H) tare Sheikh Muhammad Mahmoud Turo Kano a taron Nisfu Sha'aban na karshe kafin wakiyar Zariya.

Daga -Idishia Jos.

Yadda Sayyid Zakzaky (H) ya dauke shi kasan lallai Allah ya masa wani baiwa na musamman, shi yasa tun farko Malam ya nuna muhimmanci ko damuwa da lura akan shi Malam Turi. Nasan akwai wani lokaci da ya nuna wa 'Yan uwa cewa ya kamata duk wani abun da wani 'Dan uwa zai yi a wannan Harka in dai yana tare da Malam to kada yayi wannan abin sai ya tuntubi Malam Turi a matsayin Jagora, wannan kalman Jagora Malam (H) ya ayyana ya fara furtawa ne akan shi Malam Turi.  Ban san wani 'Dan Uwa da malam ya ambata a matsayin jagora kamar shi Malam Turi ba.

Fagen Ibada da 'dabi'u to ba'a magana na Malam Turi, to, Allah (T) ya mai baiwa da tsayawa da jajircewa wajen abinda ya shafi kyautata Alakan sa da Allah da hidimtawa addini. Rayuwan Malam Turi guda 2 ne hidimtawa addini da kuma sallamawa jagora, wannan abubuwa guda 2 shine tsayuwan Malam Turi. Don haka duk dabi'un sa da halayensa zaka ga dabi'une da halaye irin na bayin Allah na gargaru. Kuma Allah ya azurta Malam Turi da Hakuri, in ka zauna tare da Malam Turi to, lallai zaka koyi hakuri.

Kowa da kowa na Malam Turi ne, wajen Mu"amala malam Turi yana tafiya da kowa da kowa ba tare da cewa kana son shi ko baka son shi ba. Yana mu'amala da kowa ne. Dan haka kowa nashi ne, Malam Turi Yasha wahalhalu da jarrabawa amma ya nuna juriya da hakuri, Malam Turi irin juriyansu sai waliyan Allah. Babu wani wanda zai munana Malam Turi face Malam Turi bai kyautata mishi ba, kuma babu wani wanda zai zo da damuwa ba tare da Malam Turi ya biya mai bukatansa ba kuma batare da wani ya sani ba. Dabi'unsa abin koyi ne, dabi'unsa ya samu ne daga su Malam (H).

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post