Ayyukan Nisfu Rajab Da Falalolin Da Ke Ciki.

Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yana jawabi a Hussainiyyah Bakiyatullah Zariya.

Daga -Idishia Jos. 

Watan Rajab yana daga cikin watanni hudu da Allah (T) yake so a kiyaye hurumin su, ba'ason fada ko cecekuce. Watan Rajab watane mai gurma wata ne mai alfarma. Wata ne da ake so bawa ya yawaita ibadodi, har ma yazo Annabi (S) yana cewa; Watan Rajab watan Allah ne mai girma, babu wani wata daga cikin watanni da ya kusance shi wajen alfarma da daraja da falala, ayi yaki tare da kafirai a cikin watannan haramun ne.'Ala'  Ku saurara watan Rajab watan Allah ne, watan sha'aban watan nane inji Manzon (S), watan Ramadan kuma watan Al'umma tane.


Manzon Allah ya kara cewa; Ku saurara duk wanda ya azumci yini daya a  watan Rajab to yardan Allah babba ta wajaba akansa, kuma fushin Allah zai nisantu akansa Allah ba zai yi fushi dashi ba! Kuma za'a rufe kofofin wuta daga barin sa. A cikin ruwaya daga Musa Bin Jafar (As) yace; Wanda ya azumci kwana daya na Rajab, wuta zata nisanci shi tsawon tafiya shekara guda. Wanda kuma ya azumci kwana uku na Rajab Aljanna ta wajaba a gareshi.


A wani ruwaya yazo cewa Watan Rajab wata koramace a cikin Aljanna, Wanda yafi nono ko madara Haske, kuma yafi Zuma zaki. Duk Wanda ya azumci kwana daya ko Biyu na Rajab Allah zai shayar dashi daga wannan korama din.


Daga imam Jafar Sadiq (as) take cewa; Manzon Allah yace Watan Rajab wata ne na 'Istigfari' na al'umma ta don haka Ku al'ummata ku yawaita 'Istigfari'. A kalla ana son kowa ni rana idan Baka yi Istigfari' ba kayi Istigfari' Dari (100) idan zaka iya a kowanne rana kayi Istigfari' sau Dubu (1000) cikin wannan wata, domin Allah (T) mai garafane mai jin kai a wannan wata. 

A cikin wannan wata rahamar Allah ne take kwaronyowa kan Al'umman Manzon Allah (S). Ku yawaita karanta 'Astagfirullah wa Astagfirullahi Tauba' a cikin wannan wata.


Watan Rajab wata ne da Allah ya fifitashi, kuma ya girmama huruminsa, kuma Allah ya wajabta karama ga ainihin masu azumin watan. Salim yake cewa Imam Jafar Assadiq (As) shin; idan na azumci sauran abinda ya rage na wannan wata zan rabauta da wannan lada mai yawa? Sai imam Jafar (As) yace; Wanda yayi azumu a karshen wannan wata na Rajab, to zai zamo mishi aminci daga tsananin magagin mutuwa. Kuma zai zamo masa aminci daga ainihin azaba ta ranar tsinkaya da kuma azaban kabari.


Ya zo cewa duk wanda ya azumci kwana Biyu a karahen watan Rajab to zai zamo yana da 'Ticket' na tsallake siradi. Wanda ya azumci kwana uku na watan Rajab zai zamo Allah ya amintar dashi daga firgici ranar kiyama da tsanani ranar hisabi kuma za'a nesantar da shi daga wuta. Sannan kuma akwai tasbihi da ake so mutum yayi "Subahnalli'ilahil Jalil Subahana malla yan baki tasbihi illa lahu subaha la'azzal akaram subahana mallabista izza wahuwallahu ahadun."

Sannan akwai addu'oi da ake so mutum yana yi kowanne rana sun zo a cikin Mafatihul Janan akwai kuma addu'a Rajabiya da ake so shima mutum yayi suna nan sun kai wajen 8 Wanda ake so mutum yayi a wannan wata na Rajab. Sannan akwai Istigfari "Astagfirullahi lazi la'ilaha illahuwa wahdahu lasharika lahu wa'atubi ilai" sau  Dari ko "Astagfirullahi wa a tubu ilahi" ko "Astagfirullahi zaljalali wal ikram min janmi'izzunubi wal Asam".

Sannan akan so a wannan wata na Rajab ka azumci koda Alhamis da Juma'a Asabar koda ba zakayi sauran ranakun ba, kuma akwai azumin ranar 13, 14, 15, akwai du'au 'Ummu Dawud' da ake son ayi. Wanda yayi wannan azumi Allah zai bashi lada kamar ya bauta mai na tsawon shekaru Dari Tara, watan Rajab ne take da wannan falaladin
         
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.



#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post