Babban sakataren majalisar ƙoli ta tsaron kasar Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewar kamata yayi Amurka ta yi wa duniya bayanin rawar da ta taka wajen ƙirƙiro da kuma yaɗa ƙwayar cutar nan ta Coronavirus maimakon zargin Iran da China.
(Rohoton abna24.com) Ali Shamkhani ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yace maimakon zargi maras tushe kan Iran da China, kamata yayi jami’an Amurka su fito su yi bayani wa duniya rawar da suka taka wajen ƙirƙirowa da kuma yaɗuwar cutar coronavirus.
Babban sakataren majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar ta Iran ya ci gaba da cewa zargin wasu ita ce hanyar da Amurka ta ke bi wajen gudu daga ɗaukar nauyin abin da ta yi.
Ali Shamkhani yana mayar da martani ne ga kalaman sakataren wajen Amurka Mike Pompeo da yayi shekaran jiya Talata inda ya zargi kasashen China da Iran da ɓoye bayanai don gudun ɗaukar nauyin da ya kamata su ɗauka.
Kasar China dai ta zargi Amurka da ƙirƙiro cutar da Corona tana mai zargin sojojin Amurka da shigo da kwayar cutar cikin ƙasar Chinan.
Tags:
Labaran Duniya