Sadaukarwar Imam Ali (AS)!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KU SAUKA QASA KU BA SHI KARIYA

A daidai lokacin da kafiran Makkah suka gama taron sirrin makircinsu don su kashe Manzon Allah (S.A.W.W)sai Allah (T)ya umarce shi cewa yayi Hijra zuwa Madinah cikin wannan dare.

Jin wannan umarni na Allah sai shi kuma ya kira qaninsa Imam Ali (A.S)ya damqa masa dukkan amanonin da aka bashi don ya mayarwa masu ita kafin shima ya bi su. Sannan ya umarce shi kan cewa ya kwanta akan shimfidarsa cikin wannan dare.

Imam Ghazali ya kawo cikin littafinsa (IHYA'UL-ULUM)cewa, a wannan dare Imam Ali (A.S)ya kwana ne kan gadon Manzon Allah (S.A.W.W), kuma Allah yayi wahayi zuwa ga Jibrilu da Mika'ilu (A.S)cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE NI NA HADA 'YAN'UWANTAKA A TSAKANINKU KUMA NA SANYA RAYUWAR 'DAYANKU TA FI TSAHO KAN RAYUWAN 'DAYAN. TO, WANENE DAGA CIKINKU ZAI FIFITA RAYUWAR 'DAYANKU AKAN TASA?‘’

Sai kowa daga cikinsu ya zabi rayuwa kuma yafi sonta. Sai Allah yayi wahayi gare su cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ASHE BA ZA KU KASANCE MISALIN ALIYU 'DAN ABIY 'DALIB BA? NA HADA 'YAN'UWANTAKA TSAKANINSU DA MUHAMMADU, SAI YA WAYI GARI AKAN SHIMFIDARSA YANA FANSARSA DA RANSA?‘’

Sai kowa ya zabi rayuwa da kuma sonta. Sai Allah ya qara yin wahayi gare su cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ YANZU BA ZA KU KASANCE MISALIN ALIYU 'DAN ABIY 'DALIB BA? NA HADA 'YAN'UWANTAKA TSAKANINSA DA MUHAMMADU, SAI YA KWANA AKAN SHIMFIDARSA YANA FANSARSA DA RANSA, KUMA YANA FIFITA SHI DA RAYUWA? TO, KU SAUKA QASA KU BA SHI KARIYA !‘’

Jibrilu ya kasance kusa da kayin (Ali), Mika'ilu kuma yana tsaye kusa da qafafunsa suna kira (da madaukakiyar murya)suna cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ MADALLA-MADALLAH DA WANNAN MISALI NAKA YAA 'DAN ABIY 'DALIB, ALLAH NA YIN FAHARI DA KAI (yabonka) CIKIN MALA'IKU!‘’

Daga nan sai Allah ya saukar da;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ DAGA CIKIN MUTANE AKWAI WANDA YA SAYAR DA RANSA DON NEMAN YARDAR ALLAH, KUMA ALLAH MAI TAUSAYI NE GA BAYI .‘’

(BAQARA, AYA TA 207)

-NURUL-ABSAR, SH:140.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

              09039791509

~13th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post