RA'AYINA DANGANE DA (CORONA VIRUS)

RA'AYINA DANGANE DA (CORONA VIRUS).

Wannan Ra'ayina ne dangane da annobar dake addabar Duniya a yanzu wato cutar (Corona Virus), bai kamata ace annoba tazomana a Duniya ace mubar Ibada ba! ko ace mubar haduwa Masallatai na Juma'aba sakamakon wanna cutar, abinda ya kamata 'yan uwana Musulmai su fahimta rayuwa da mutuwa duk na Allah ne Lokacin da yasu haka ya yakeyi.

Minene dalilinda zaisa kabar zuwa Masallaci, duk inda al'umma suka hadu sukayi addu'a take Allah ke amsa madamar mutanen sunkai (40) domi cikin mutanen baza'arasa wanda Allah kejin maganarsa ya amsa.

Idan akabar Taruwa Masallaci to Kasuwafa da Ofis ko shiga motoci fa dole Al'umma suyi cudanya da juna ta fannoni daban-daban.

Ya kai dan uwana Musulmi idan kabar masallaci dakin Allah inane zaka gayama Allah matsalarka ya magancema wajibinmu ne mu Musulmai mushiga taitayinmu rokon Allah dare da rana, Gida da masallaci, Ofis da Kasuwa, kada mu manta akan makircin Yahudawa dangane akan addinin Muslunci.

A nawa ra'ayin ba mafita bace ace ankulle Masallatai ko a hana ziyartar dakin Allah wajen Aikin Hajji, miyasa idan shuwagabanninmu nada wasu bukatu suke biyawa mutane aikin Hajji domin rokon Allah ya biyamasu bukatunsu sai mu da annoba ta addaba ace kada muje a'a wannan ba uzri bane  anawa ra'ayin.

Ba mafita sai mun koma ga Allah. Ya Allah ka iya mana abinda bamu iyawa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post