MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Daga: Bin Haroun Sigau
Arsenal ta ce Marinakis mai shekara 52, ya hadu da wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar lokacin da Gunners din ta karbi bakuncin kungiyar Girka a wasan Europa mako biyu da suka gabata.
A ranar Talata, Marinakis wanda shi ne mamallakin kungiyar Notteingham Forest, ya ce an gwada shi kuma ba ya dauke da cutar ta Covid-19.
Yanzu dai Olympiakos za ta karbi bakuncin Wolves ranar Alhamis a wasansu na Europe
Uefa ta ki amincewa da bukatar Wolves ta a daga wasan saboda tsoron coronavirus.
Hukumar Premier ta ce ana daukar duk wasu matakai da suka dace na kariya.
Brighton ta ce wasanta da Arsenal ranar Asabar za a yi shi ne babu 'yan kallo.
Rahotanni na cewa ya zuwa yanzu akwai mutum 382 da suka kamu da cutar a Burtaniya, kuma tuni wasu shida suka mutu.
Tags:
Labarin wasanni