MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Abbagano ✍️
( قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ )
يونس (58) Yunus
Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.
Daliban dake karatu a JAMI'A da HAUZA a Niger ne suka tsara kayataccen mauludin sayyida Zahara da imam Ali (as)
Mauludin gaskiya ya kayatar sosai da sosai, domin ankere mahallin program din sosai, ta yadda zakaga gun yadau wani kwalliya da kyalkyali Mai kayatar wa, Hadi da balanbalan Mai kyau sosai, sannan ga wani shinfidadden kafet. Na shigowar malamai.
Taron yasamu halartar manyan baki daga cikin garin nermay Niger, dakuma wasu daga cikin malamai da daliban jami'a da hauza maza da mata.
Malama halima ta gabatar da jawabi kan sayyada Zahara (as) inda ta tabo bangarori da Daman gaske kan sayyada Zahara.
Babban shehin Nan na kasar Niger (sheak salihu Lazare) shine ya gabatar da jawabi kan imam Ali (as) a filin taron.
( وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ )
الضحى (11) Ad-Dhuhaa
Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).