Nifa kaina ya ɗaure akan matashin da aka ce yayi ɓatanci ga Fiyayyen halitta (s.a.w.w)



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

A dazu da Ina cikin daki a kwance sai abokina Sani. Yake cemin tashi ka samo rahoto. Sai nace dashi miye yake faru ? Kafin ya fara fadamin ,kawai sai naga mutane suna ta gudu zuwa wani layi dake a bayan gidan mu. Dake a cikin Unguwar Dabai, a karamar hukumar gwale, Kano.

Ai kuwa nima ban tsaya ba. Sai na bisu domin gani da idanuwa na. Ina zuwa ta bayan layin kawai sai naci karo da motocin Yansanda guda uku. Duk a cike suke da Yan sanda. Su kuma daga Mai binda sai mai sanda. Suka you cikin mutane da gudu. Inda suna isa cikin taron mutanen suka fara harbi a sama. Ni kuma na bi Yan sanda a baya. Domin ganin abinda yake wakana a wurin. Yan sandan da suka fara harbi a sama suka ga mutane suna ta kabbara(Allahu Akbar ). Sai wani yake cewa yallabai kada kuyi duka. Domin kuma bazaku ji da Dadi ba. Jin haka yasa yan sanda suka. Dakata da harbi a sama da kuma niyyar su ta yin duka a wurin.

To a lokacin na hangi kofar gidan Limamin Unguwar Dabai din ne. Matasa suke kokari da karfin tsiya sai sun shiga. To kafin na karasa wurin saboda taron jama'a yayi yawa. Sai nake ji wasu suna cewa " wallahi sai mun kasheshi." Sai nake tambayar wani cewa miye yake faruwa? Sai yake cemin "ai Dan gidan Limamin Unguwar Dabai yayi batanci ga Annabi (S.A.W)."  To da jin haka sai na ce Subhanallah ! Kawai sai naje gaba. Domin dauko hotuna da bidiyon.

To bayan da na karasa kofar gidan, sai naga Yan sanda suna ta kokawa da mutanen wurin. Wato Yan sandan sun hana Matasan Shiga gidan. Su kuma Matasan  suna ta cewa Wallahi An dai na taba Martabar Manzon Allah a Kano akwana lafiya. Yan Sandan sun tattare kofar gidan cewa lallai baza a shiga ba. Su kuma al'umma suna jifa, da duwarwatsu hade da Kabbara. Har ta kai ga Matasan suna kokrin fin karfin Yan Sandan. To a lokacin ne Yan Sandan suka fara harbi a sama domin a gudu. Amma abin mamaki hatta da kananan yaran da suke a wurin ko gezau basa yi. Sai da kawai kaji Kabbara na tashi (Allahu Akbar).

Kai ! Abin fa har sai da ya gagari Yan sandan . A gaban su aka fara rushe ginin gidan. Tare da haurawa ta makwabta. Aka kunnawa gidan wuta Yan Sandan suna kallo. To a lokacin ne suka kira domin a karo musu sauran karin jami'an tsaron. Hade da motar yan Fire Service (masu kashe gobara). Kafin su karaso an kone gidan. Kuma suka hana a motar kashe wutan taje wurin. Sannan Kuma Suma jami'an tsaron aka raka su da gudu.

To , ban Matasan sun yi wannan jahadin kamar yadda suke cewa. Sai kuma suka ce to fa yanzu duk gidan wanin. Shehin na su Yan  Faira (Yan hakika) sai sun koma shi. Haka kuwa suka je gidan Karmawi da Kuma shehu Malam Nazifi. Inda suka fara saukar da rufar kofar gidan. To a nan ne fa jami'an tsaron suka zo da karfin su. Suna ta harba Barkon tsohuwa (Teagas). To Nan ne fa masu jahadi suka fara gudun ceton rai. Inda har yanzu akwai jami'an tsaron a kofar gidan Shehu Malam Nazifin.

Sai dai nayi iya kokarin ganin Wanda ya ga ko yaji abinda shi wannan matashin ya fada. Duk da dai wasu sun ce min wai a group din what's app ne yayi batancin. Wasu Kuma suka ce a shafin sa me na sada zumunta na Facebook ya wallafa hakan. To duk dai nayi kokarin ganin hakan amma ban samu. Amma insha Allah zamu cigaba da bibiyar lamarin.

Wannan shine abin da ya wakana yau Assabar 28/3/2020. A Unguwar Dabai dake a karamar hukumar gwale dake a cikin Garin Kano.

~Auwal M. Tukur
28/3/2020

Ga hotuna nan a kasa






Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post