Neman kashe Sayyid Zakzaky, da sunan Coronavirus a gidan yarin Kaduna




Daga Bin Haroun Sigau                                           

Rahoton da yake shigo mana a halin yanzu shine gidan yarin Kaduna inda anan ne azzaluman mahukunan Nigeria suke tsare da sayyid Zakzaky {h} ba lafiya a halin yanzu.

Wanda kuma a fahimtar mu su azzalumai suna so suyi amfani da sunan Coronavirus su kashe jagoran harkar musulumci Sayyid zakzaky (H)

 Kamar yadda muka samu daga cikin gidan yari din a halin yanzu su y'an gidan yari din sunata faman ihu ne a sakamakon fitar da wata mata wanda sukace takamu da wannan kir kirarriyar cuta.

Haka a yauma wai sun fidda wata mace guda daya wai itama takamu da wannan cuta. don haka a halin yanzu ma su mazauna gidan yarin sun fara karya kofofin dakunan su sun taru a tsakiyan gidan.

Harma sunyi wa DC wanka da miyan kuka. don haka yana dakyau y'an uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) na ko ina a fadin duniya su san halin da ake ciki kuma muyi dukkan me yuwuwa. muna rokon Allah ya bawa su Sayyid Zakzaky (H) lafiya .

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post