MATASAN MU A YAU!!!
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Zae
nabal haura'a ubale✍️
part (1)
Bayan gõdiya ga ubangijin matasa, Wanda shine mahalaccin dukkanin matasa,Wanda yake da iko abisa kan dukkanin matasa.
Na zabi nayi rubutu ne don tinatar wa bisa halin da 'Yan uwana matasa muke kai, Wanda hakan ya sabawa koyarwar shugaban matasa annabi Muhammad (s),hakan yasa nayi yinkurin wannan tunatar wa gare mu matasa, domin tunatar wa Tana anfanar mumini.
( وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَىٰ تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ )
الذاريات (55) Adh-Dhaariyat
Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai.
Nazabi nayi wannan rubutu ne don fadakar wa da tunatar wa garemu matasa,tare da misalta fadin manzon Allah (s) dayake cewa
ﻣَﻦ ﺭَﺃَﻯ ﻣِﻨﻜُﻢ ﻣُﻨْﻜَﺮًﺍ ﻓَﻠْﻴُﻐَﻴِّﺮْﻩُ ﺑﻴَﺪِﻩِ، ﻓﺈﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﺴْﺘَﻄِﻊْ ﻓَﺒِﻠِﺴﺎﻧِﻪِ، ﻓﺈﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﺴْﺘَﻄِﻊْ ﻓَﺒِﻘَﻠْﺒِﻪِ، ﻭﺫﻟﻚَ ﺃﺿْﻌَﻒُ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ.
ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ﺍﻟﺼﻔﺤﺔ : 49
Wanda yaga Abu mummuna, to yacanja shi da hannun sa,Idan bazai iyaba, to yacanja da harshen sa, Idan yagaza to yacanja da zuciyar sa, duk da yake hakan shine mafi rauni a imani.
Toni nazabi nayi magana bisa kannawa sauyin ta hanyar anfani da harshe Wanda shine abinda Zan iyayi.
Wannan hadisi Yana daga cikin dalilan dayasa nazabi nayi wannan rubutun,domin gaskiya halin da muke Kai a yanzu yayi Muni sosai.
Dayake wannan shine rubutun farko, shiyasa nake rokon ku,da kibuyo ni don samun cigaban rubututtakan, don Zan rarrraba shine,gudun karna gajiyar da Mai karatu.
Kayi kokarin bibiya don Kila ka anfana da daya daya cikin maganganu na,
( الَّذِينَ يَسْتَمِعُونَ الْقَوْلَ فَيَتَّبِعُونَ أَحْسَنَهُ ۚ أُولَٰئِكَ الَّذِينَ هَدَاهُمُ اللَّهُ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمْ أُولُو الْأَلْبَابِ )
الزمر (18) Az-Zumar
Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali,
Malaman hikima sunace wa: mafi hikima cikin mutãne shine Wanda inyaji abunda zai anfane shi yayi kokarin aikata wannan abin.
Mu hadu a kashi na biyu