Ma'asumah Nigerian News Update
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_Zaenabal haura'a ubale ✍️_
_WANE NE MATASHI?_
Duk da yake kalmar matashi abune Wanda kusan kowanne mu yasani, amman hakan bazai hana mu muyi bayani ba.
Matashi muna iya cewa shine: Wanda ya mallaki hankalin kansa, yake da cikakken ikon Yi ko Bari, bisa radin kansa, yasan dai dai yasan badai dai ba, sannan shekarun sa suka Kai akalla daga 14 zuwa sama, ta yadda muna iya cewa yazama mukallafi.
Wanda yasamu cikakken iko a hannun sa, lalle muna iya Kiran sa matashi, duk da bawai samun ikon ne kadai ma'anar matashi ba, amman de Yana daga cikin abubuwan da suke taruwa su bada matashi.
Yaya halin matasan mu ta fuskacin ilimi? Nasan tabbas akwai matsala babba ba karama ba. Don halin da muke Kai yanzu hakika abin takaici ne, don zakaga kusan matasan ko wacce kasa sama suke da matasan mu.
Tabbas matasa sune kashin bayan kowanne abu, Wanda duk abinda da kaga matasa sun tsayu dashi zakaga abin Yana cigaba sosai, amman dazarar kaga babu matasa ciki, to lalle babu wani fata ga wanna abin.
Yanzu ta fuskacin ilimi ko'ina ancigaba anbar mu abaya, Wanda mune yakamata muzama a gaba' tunda mune addinin mu yagaya mana cewa:
(ﻃﻠﺐ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻓﺮﻳﻀﺔ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﻣﺴﻠﻢ)
_Neman ilimi wajibi ne akan kowanne muslimi._
_1- Matasa sune goben ko wacce al'umma,iyaye ga al'umma mai zuwa,Wanda tarbiyar al'ummar gaba yake hannun su,ta yadda zasu sauya ta zuwa duk halin da suka ga dama._
_2- gyaruwar matasa,gyaruwar al'umma ne, haka 'bacin su bacin dukkanin al'umma ne, domin sune karfin Nan Mai motsi cikin al'umma._
_3- cikar al'umma Yana hannun matasa,Kamar yadda sauyin su yake a hannun matasa,Wanda idan sun sauyasu a hanyar Allah to al'umma sun gyaru._
Allah yabamu labarin al'ummun baya a alkur'ni domin yazama izina garemu.
( لَقَدْ كَانَ فِي قَصَصِهِمْ عِبْرَةٌ لِّأُولِي الْأَلْبَابِ)
يوسف (111) Yusuf
_Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali._
Jin kissosi wadanda suka gabace mu, ba komi bane sedan mu samu abin koyi, Kamar yadda Allah yagayawa annabin sa.
( أُولَٰئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللَّهُ ۖ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهْ)
الأنعام (90) Al-An'aam
_Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu._
*_Mu hadu a rubutu na gaba_*