Matar Firai Ministan Canada ta kamu da coronavirus




Sophie Grégoire Trudeau, matar Firai Ministan Canada Justin Trudeau ta kamu da cutar coronavirus, in ji wata sanarwar ofishin firai ministan

Daga -Idishia Jos

"Za a ci gaba da kebe ta a yanzu. Ta samu sauki kuma tana daukar matakan da suka kamata," a cewar sanarwar.
A halin yanzu, firai ministan da matarsa sun kebe kansu.


Ofishin Mista Trudeau sun fitar da sanarwar cewa firai ministan na cikin koshin lafiya kuma ba shi da wasu alamu na cutar, amma zai ci gaba da keba kansa tsawon mako biyu.
Amma ba za a yi wa Mista Trudeau gwajin cutar ba tukuna.

Ma'aikatan lafiya za su nemi mutanen da suka yi mu'amala da Misis Trudeau kwanan nan.


Amma ba za a nemi wadanda suka yi mu'amala da firai ministan ba saboda har yanzu bai nuna alamun cutar ba.


'Yan siyasa a fadin duniya na ci gaba da killace kawunansu a 'yan kwanankin nan ciki har da manyan 'yan jam'iyyar Republican biyar na kasar Amurka da wani ministan Canada.


An dage duk wasu taruka da ya kamata Mista Trudeau ya halarta kwanan nan, amma zai gudanar da wasu tarukan nasa ta wayar tarho inda za a tattauna matakan da ya kamata kasar ta dauka kan annobar, a cewar wata sanarwar ofishinsa.


Kawo yanzu a kalla mutum 103 ne suke dauke da cutar a Canada, a lardunan British Columbia da Ontario da Alberta da Quebec da Manitoba. Mutum daya ne ya mutu sanadiyyar cutar kawo yanzu a kasar.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post