Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani ★Part5★



MA'AUNIN HANKALI
MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Tare da: Abba Gano

(Tattaunawata da wani dan uwa)).
__________________________________
__________________________________
★MACE DA NAQASUN HANKALI★

Sunce mace tanada tawayar hankali saboda ko a Kotu shaidar mace biyu takeyin daidai da shedar namiji daya.Wallahi nidai bansan alakar wannan da hankali ko naqasunshi ba.

★ WARWARE SHUBUHA★
1- Farko dai wannan hujja bata dogara da Alkur'ani ba, sannan taci karo da abunda Alkur'ani ya fadi. A lokacin da Allah ta'ala ya fadi cewa shedar mace biyu a madadin namiji daya take, ai ya fadi dalili, miyasa kuka tsallake dalilin alkur'ani kuka dauki na ruwayar da ba'asan ingancinta ba??. Allah ta'ala yace: ﺃَﻥ ﺗَﻀِﻞَّ ﺇِﺣْﺪَﺍﻫُﻤَﺎ ﻓَﺘُﺬَﻛِّﺮَ ﺇِﺣْﺪَﺍﻫُﻤَﺎ ﺍﻟْﺄُﺧْﺮَﻯٰ
Adalili shine {{KODA DAYA TA MANTA SAI DAYAR TA TUNA MATA}}.
Aya tace mantuwa ko dimuwa (Da karinar ( ﻓﺘﺬﻛﺮ) Hadisi yace A'a tawayar hankaline ya sanya hakan. To wane zamudauka kenan? koko akwai wanda zai ceman Mantuwa daga tawayar hankali take?? inkuwa daga karancin hankalo mantuwa take to har mazanma bazasu fita ba, domin suma suna mantuwa.
Abunda yasa mace zata iya mantawa kota rude kota dimauce a gaban kotu shine : Ita abisa yanayin halittarta bata cika shiga rintsi ko tashin hankali ba, a rayuwa, koda yaushe ana bata kariya ne, shiyasa bata shiga fagen fama tai yaqi, saboda haka mai sauki ne idan ta tsaya gaban alqali ta firgice ko hankalinta ya tashi harta manta abunda zata fada. Amma ba karancin hankaliba kamar yanda kukace.
Sabnin namiji wanda koda yaushe cikin gwagwarmayar rayuwa yake a gida da waje, ya saba da irin wadannan matsaloli, shiba karamin abune zai tada mashi hankali ba. Kuma yanayin halittarshi ma , tana iya jure abunda halittarace bazata iya jurewa ba. Amma dukda haka yana iya rikicewa a gaban alqali to inaga mace??.
Cigabanshi yana kashi na 6

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post