Mata ba masu raunin hankali bane, bare na Imani ★Part4★




Ma'asumah Nigerian News Update

MA'AUNIN HANKALI

Abbagano

(Tattaunawata da wani )).
__________________________________
__________________________________
2- Idan har rashin yin ibadu saboda larurar HAIDHA ya zama naqasu a addinin mata, to har mazan ma ta shafa.
Shin Naqasu ne idan matafiyi yayi sallah raka'a biyu a madadin hudu?? Shi naqasu ne ga matafiyi kowa na azumi amma shi bayayi??. Kamar yanda addini ya umurci Matafiyi yayi kasaru, sannan ya ajiye azumi saboda samun sauki, haka Allah ya umurci mace ta ajiye azumi da Sallah saboda samun saukin halin datake a cikinsa na rashin lafiya.
3- Sannan tayaya umurnin Allah da manzo zai zama naqasu a addini?? Ashe ba Annabi ne ya umurcesu da ajiye azumi da Sallah ba?? to tayaya kae tsammanin zai dawo yana fada masu cewa hakan naqasu ne?? Kenan annabi shine ya haifar masu da naqasun tunda shiya hanasu??.
4- Sannan tayaya mace mai naqasun addini zata kasance farkon wadda ta fara bada jininta domin addini ya daukaka, dukkan wanda ya karanta tarihin musulunci yasan wannan.
5- A takaice bancema babu mace mai naqasun Addini ba, amma bazai yiwu kayi UMUMI kace baki daya haka suke ba. kamar yanda suke da masu naqasun addini haka sukeda masu cikakken addini.
kamar yanda maza suke da masu cikakken addini haka suke da masu naqasun Addini.
mu hadu a kashi na kashi 5

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post