@Ma'asumah Nigerian News Update@
Abbagano
MA'AUNIN HANKALI DA ADDINI
_Tattaunawar mu da wani dan uwa_
A DOKAR HANKALI.
Idan Mutum yace bai yarda da abu ba, to kamata yayi ka tabbatar mai da wannan abun kafin ka fara zaginshi da nuna cewa yayi ba daidai ba.
Hatta kafurai basu zama kafurai ba, saida aka bayyana masu gaskiya da hujjoji yankakku, suka gani, suka gane, suka kauda kai, daganan suka zama kafurai. Amma kafurin da hujja bata zomashi ba wannan ko azaba bazata shafeshi ba.
..... ﻭَﻣَﺎ ﻛُﻨَّﺎ ﻣُﻌَﺬِّﺑِﻴﻦَ ﺣَﺘَّﻰٰ ﻧَﺒْﻌَﺚَ ﺭَﺳُﻮﻟًﺎ
ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ ( 15 )
....BAMU KASANCE MASU YIN AZABA BA HARSAI MUN AIKO WANI MANZO.
Amma yanzu wai mutum daya gayama abu kace baka yarda ba, saidai kaji sunanka a kasuwa yana yayataka cewa wai baka yarda da kaza ba , kuma bai kawo maka hujja ko daya ba wadda zata sanya ka yarda da wannan abun.
Bisa misali , inda wani zai kawo maka wani hadisi, yace wai annabi yace kaza, Idan kace baka yarda da wannan hadisin ba, saidai kaji ana yada sunanka a matsayin wai kana karyata annabi. Alhali inda za'a kawoma hujjoji cikakku dazasu tabbatar da cewa wannan hadisin annabi ne, da wuri zaka karba ,kuma ka aikata.
A lokacin da wani yace bai yarda da hadisi kaza ba, to ba yana nufin ya karyata zancen Annabi bane, a'a bai yarda annabi ya fadi bama tun asali, idan kanaso ya yarda tosai ka kawo hujjojin dazasu tabbatar da cewa annabin ne ya fadi dagaske. Tunda ai kowa ya sani anayiwa annabi karya ,ace yace alhali baice ba. tun zamaninshi, ballantana Shekaru sama da dubu bayan wafatinsa.
Larabawa suna cewa :
ﺛﺒﺖ ﺍﻟﻌﺮﺵ ﺛﻢ ﺍﻟﻨﻘﺶ .
Gado ake fara samarwa sannan aimai kwalliya. Amma yanzu mutanenmu Kwalliyar suke nema suyi alhalin babu gadonma.
Da farko na lura akwai nau'i na MUGALADA a cikin bayaninka, bari in kara fitoma da abun a fili kafin mu cigaba.
Niba ina magana akan asalin TASHRI'I bane, ina magana akan hukunci bayan tashri'i.
Magana akan asalin tashri'i wannan banida zabi a cikinsa. Saboda ubangiji ne mai shari'a, shiyake sanyata a yanda yaso. Ammafa ka sani cewa idan ya sanya shari'a to wurin hukunci yanayin adalci ne.
Maganar Auren mata 4 ga namiji, da amsar rabon gado kaso biyu ga namiji, da maganar Saki a hannun namiji. wannan duka Tashri'i ne. Kuma Allah ne yaga dama ya sanyasu a haka.
Amma hakikanin abunda nake cewa shine, idan Allah ya hukunta abu sannan wani ya aikata, bazai yiwu kuma yace wannan aikin nakasu bane.
1- Misali shine ya hukunta mace ta auri namiji daya, amma bazai yiwu Allah yace saboda Tanada nakasu ba. A'a saboda haka yaga dama. Bisa wasu hikimomi wanda badon gudun Fita daga maudu'i ba dana kawo su.
2- Sannan Maganar Amsar rabin gadon namiji ga mace , wannan ma haka Allah yaga dama, Amma idan mace tabi wannan hukunci na Allah , ta amshi rabin gado bazai yiwu kuma yace wannan nakasu bane. Tattare da cewa ba ko ina bane mace take amsar Rabin gadon namiji. Akwai lokacin da mace take amsar gado daidai da namiji, akwai lokacinda mace take amsar gado fiye da namiji, kamar yanda akwai lokacinda mace take amsar gado Rabin na namiji. Gadukkan wanda ya karanci rabon gado yasan wannan.
Idankau Har Allah zai sanya shari'a sannan ya siffanta masu biyayya ga shari'arshi da nakasu, kenan yana umurni da nakasu ne.
A takaice abunda nake cewa shine :(( Idan Allah ya sanya shari'a , sannan aka samu mace tayi biyayya ga wannan shari'ar , to bazai yiwu a siffanta ta da nakasu ba)) Yin hakan kamar siffanta Shari'ar Allah ne da nakasu.
Sannan kullum kokari kake kace Allah yanayin abu cikin hikima, amma a magana kana warware kanka.
ka gaya mani miye hikima a cikin yanke wannan hukuncin ( Marar lafiya da matafiyi da Mai haidha ya wajaba su ajiye azumi) amma dukkansu idan sun ajiye babu nakasu saidai mai haidha kawai. ?? Shin miye ya bambamta azuminsu da nata??
Dadai sauran misalan daka kawo.
Amma maganar cewa in cire hankali daga harkokin Addini, saboda hankalina baya iya fahimta, wannan kamar kana warware Addinina ne, domin Ka gayaman cewa dami kafuri zai fahimci cewa wannan shine annabin da aka aiko mashi?? Idan babu hankali hatta shari'arma bata hawa akan mutum. To idan akwaishi kuwa aiki das
hi shine aula.
Na sani malam yasan cewa Shi'a sun yarda da wannan ka'idar cewa :
ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﻘﺒﺢ ﻋﻘﻠﻴﺎﻥ .
kuma wannan shine bambamcin shi'a da 'yan ASH'ARIYYA su suna cewa
ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﻘﺒﺢ ﺷﺮﻋﻴﺎﻥ .
Nidai a iya sanina malam Usman dan shi'a ne, bansan yaushe ya kaucewa shi'a ya dauki ra'ayin Ash'ariyya ba.
Da ace babu hankali a shari'a da Allah baice :
ﻛَﺬَٰﻟِﻚَ ﻳُﺒَﻴِّﻦُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻟَﻜُﻢْ ﺁﻳَﺎﺗِﻪِ ﻟَﻌَﻠَّﻜُﻢْ ﺗَﻌْﻘِﻠُﻮﻥَ
Allah yana bayyana mana ayoyinsa ne saboda mu hankalta, Amma malam kana ceman wai in ajiye hankali gefe, to wace maganar zan dauka? taka kota alkur'ani?
sannan ita kanta maganar ta cewa Hankalina bazai iya gane komai ba, ai daga hankali ka samota, domin babu aya ko hadisi da suka nuna hakan.
Idan zan ajiye hankali ya zanyi da wannan ayar :
ﻛِﺘَﺎﺏٌ ﺃَﻧﺰَﻟْﻨَﺎﻩُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ﻣُﺒَﺎﺭَﻙٌ ﻟِّﻴَﺪَّﺑَّﺮُﻭﺍ ﺁﻳَﺎﺗِﻪِ ﻭَﻟِﻴَﺘَﺬَﻛَّﺮَ ﺃُﻭﻟُﻮ ﺍﻟْﺄَﻟْﺒَﺎﺏِ
ﺹ ( 29 )
Gashidai Allah ya saukar mani da littafinsa domin inyi tunani, tunaninma a cikin ayoyinsa, amma malam yana ceman in ajiye hankali gefe.
sannan ya zanyi da wannan ayar:
( ﺃَﻓَﻠَﺎ ﻳَﺘَﺪَﺑَّﺮُﻭﻥَ ﺍﻟْﻘُﺮْﺁﻥَ ﺃَﻡْ ﻋَﻠَﻰٰ ﻗُﻠُﻮﺏٍ ﺃَﻗْﻔَﺎﻟُﻬَﺎ )
ﻣﺤﻤﺪ ( 24 )
sannan yazanyi da wannan ayar:
ﻭَﻣَﺎ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎ ﻣِﻦ ﻗَﺒْﻠِﻚَ ﺇِﻟَّﺎ ﺭِﺟَﺎﻟًﺎ ﻧُّﻮﺣِﻲ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﻓَﺎﺳْﺄَﻟُﻮﺍ ﺃَﻫْﻞَ ﺍﻟﺬِّﻛْﺮِ ﺇِﻥ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﻟَﺎ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ ★ ﺑِﺎﻟْﺒَﻴِّﻨَﺎﺕِ ﻭَﺍﻟﺰُّﺑُﺮِ ﻭَﺃَﻧﺰَﻟْﻨَﺎ ﺇِﻟَﻴْﻚَ ﺍﻟﺬِّﻛْﺮَ ﻟِﺘُﺒَﻴِّﻦَ ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﻣَﺎ ﻧُﺰِّﻝَ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﻭَﻟَﻌَﻠَّﻬُﻢْ ﻳَﺘَﻔَﻜَّﺮُﻭﻥ
Ayoyi cike da alkur'ani wanda suke magana akan tadabbur a cikin ayoyin Allah ta'ala.
Nasan zaka iya cewa ayoyin da ake nufi sune kamar halittunsa dadai sauransu, shiyasa ban dauko ayoyin da suke magana akan wannan ba, saina dauko masu magana akan. addinin dakanshi.
Inkau maganar hadisai ake to wannan Kasan hadisin Imam Sadiq wanda yazo a cikin littafin AL-KAFI a kitabul-aql, wanda imam yake cewa :
HAKIKA ALLAH YANADA HUJJOJI BIYU A CIKIN BAYINSA, HUJJA BAYYANANNIYA DA HUJJA BOYAYYA. HUJJA BAYYANANNIYA ITACE ANNABAWANSHI, HUJJA BOYAYYA KUWA ITACE HANKALI..........
Har zuwa karshen hadisin
To yaushe Zanbar aiki da wannan ayoyi da hadisai saboda abunda kake hasashe?.
Sannan ina rokonka idan kasan wata aya ko wani hadisi ingantacce wanda yake cewa : mu daina sanya tunani a harkokin addini, ka kawo manishi domin in gyara tafiyar addini na.
Saboda haka koda ace tunanina karami ne, to Allah yana bukatar inyi aiki dashi. ba kamar yanda kake tsammani ba.
Maganar Kiyasi kuwa to nasan abun ya shigema duhu ne, domin dukkan wanda yasan hanyoyin ilimi a duniyar nan bai kamata yayi wannan maganar ba.
Inaso ka gayaman ilimi kwara daya, kona addini kona boko wanda tushenshi ba bisa kiyasi aka dorashi ba.
Inda babu kiyasi saidai muce babu ilimi.
Nasan kila kana tsammanin kiyasi irin na ilimin Usul nake nufi, to samsam badashi nake ba. Shiyasa tun a farkon maganata kaji ina cewa ((KIYASI NA MANDIK) Saboda bakada inda babushi ko a alkur'ani ko a hadisi ko a ilimin zamani. kai indai babu kiyasi irin na mandik saidai kace babu ilimi kawai, ko kuma ilimi zai zama shirme ne.
KIYASI a isdilahin Ilimin Usul yasha bambam da KIYASI a isdilahin ilimin mandik, kuma ina kyautata zaton malam yasan wannan.
A mandik idan akace kiyasi ana nufin
ﺗﻄﺒﻴﻖ ﺍﻟﻘﺎﻋﺪﺓ ﺍﻟﻜﻠﻴﺔ ﻋﻠﻰ ﺟﺰﺋﻴﺎﺗﻬﺎ ﻟﻤﻌﺮﻓﺔ ﺃﺣﻜﺎﻣﻬﺎ .
Amma a Usul idan sukace kiyasi suna nufin :
ﺇﺛﺒﺎﺕ ﺣﻜﻢ ﺍﻟﺠﺰﺋﻲ ﻟﺜﺒﻮﺗﻪ ﻓﻲ ﺟﺰﺋﻲ ﻣﺸﺎﺑﻪ ﻟﻪ .
Shiyasa a shi'a bamuda kiyasi, saidai AQAL. (Harna tuna maganar hankali , ashema dayane daga masadir na tashri'i).
Allah ya datar damu.
Daga karshe zance maka : Duka wadannan abubuwan daka lissafo a sama akwai hikimar da Allah ya sanyasu a yanda suke, kuma inadasu a rubuce, saidai kasantuwar sun fita daga maudu'inmu shiyasa ban kawosu ba.
Amma maganar rashin amsa mani tambayoyina dakai, gaskiya ban fahimci dalilin hakan ba. Ina bukatar karin bayani