MACE A MA'AUNIN HANKALI DA ADDINI
Abbagano
Tattaunawar mu da wani
Sunyi kokarin su nuna mace a matsayin wata halitta mai naqasu a asalin halittarta a Hankali da addini, bisa dogaro da hadisan da koda mun kauda kai daga sanadinsu bazasu inganta ba.
Nasan Malam yasan yanda Ahlul baiti suka koya mana yanda zamui mu'amala da Hadisi idan aka dangantashi da a'imma (as). sunce mu maidashi ga Alkur'ani idan ya dace to nasu ne, idan ya saba mashi kuwa to basune suka fadeshi ba. kuma wannan shine ya dace da ma'aunin Hankali.
To ina fatan cikin wannan tattaunawa malam zai biyoni yaga yanda hadisin nan zai karyata kansa gaba-bayan gaba. Jumla-jumla.
★DALILAN CEWA MACE NADA NAQASUN ADDINI★
Mace tabada naqasu a addini saboda idan tana Al'ada (Haidha) bata sallah dadai sauran ibadodi , hakanan wai annabi yace Sune mafi yawa a Wuta a ranar alqiyamah.
★WARWARE SHUBUHAR★
1- Asali ita al'ada wadda mata sukanyi batada alaqa da TASHRI'I, Al'amari ne TAKWINI (nasan kuwa malam yasan banbanci tsakanin biyu din). Haka Allah ya haliccesu kuma basuda zabi.
Al'ada cuta ce, ko ince rashin lafiyace kamar yanda yazo a cikin alqur'ani cewa :
( ﻭَﻳَﺴْﺄَﻟُﻮﻧَﻚَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤَﺤِﻴﺾِ ﻗُﻞْ ﻫُﻮَ ﺃَﺫًﻯ ﻓَﺎﻋْﺘَﺰِﻟُﻮﺍ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀَ ﻓِﻲ ﺍﻟْﻤَﺤِﻴﺾِ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻘْﺮَﺑُﻮﻫُﻦَّ ﺣَﺘَّﻰٰ ﻳَﻄْﻬُﺮْﻥَ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﺗَﻄَﻬَّﺮْﻥَ ﻓَﺄْﺗُﻮﻫُﻦَّ ﻣِﻦْ ﺣَﻴْﺚُ ﺃَﻣَﺮَﻛُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻳُﺤِﺐُّ ﺍﻟﺘَّﻮَّﺍﺑِﻴﻦَ ﻭَﻳُﺤِﺐُّ ﺍﻟْﻤُﺘَﻄَﻬِّﺮِﻱ
ﻥَ )
ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ ( 222 )
Nasan malam yasan ma'anar kalmar ﺃﺫﻯ
wato (cuta) ko
( ﺿﺮﺭ) ,
Kuma bansan yanda akai cuta ta zama aibi ba.
Rashin yin Sallah ko wasu Ibadu saboda lalurar (HAIDHA) shima wani nau'ine nabin Umurnin Allah, domin bawai bata iya yin ibadun bane, , a'a hanata akayi kuma ta hanu, tabi umurni.
Bansan yaushe bin Umurnin Allah ya zama naqasu ba a addini??.
Cigaban Hujjojin nanan tafe insha Allahu. Mu hadu a kashi na uku