@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
A irin wannan rana ce 13 ga Rajab, shekara 30 bayan shekarar Giwa aka haifi mai shiryarwa bayan Manzon Allah, wato Imam Ali (A.S).
An haife shi cikin dakin Ka'abah mai tsarki, kuma ya fado qasa yana mai yin sujadah ga Allah mahaliccinsa.
DARAJARSA
Sayyidah Maryam (S.A)mahaifiyar Annabi Isah Almasihu (A.S)ta kasance mai yawan ibada Zwacce ta tare cikin Masallaci kawai don bauta. Saboda kusancinta ga Allah har ciyar da ita ake yi ba tare da ganin mai zuwa mata da wannan abincin ba.
Abincinta ya kasance yana zuwa ne kai tsaye daga Allah wanda ake kawo mata daga gidan Aljannah.
To, a daidai lokacin da haihuwar Isah (A.S)tazo sai Allah ya umarceta da cewa ta fice daga cikin wannan masallaci zuwa qarqashin wani kututturen Dabino.
Ita kuma Fatimatu Bnt Asad, wato mahaifiyar mai shiryarwa a bayan Annabi (S.A.W.)Imam Ali Allah ya karrama fuskarsa(K.L.W)ta kasance a wajen masallacin ne(out of the mosque), amma da haihuwar Imam Ali (A.S)tazo sai Allah (T)ya umarceta kan cewa ta shiga cikin masallaci ta haife shi a ciki.
Kafin shi ba a samu ba, haka ma bayansa ba a taba samun wanda aka haife shi cikin qwaryar dakin Allah ba. Tabbas, wannan matsayi ya kai matsayi!
MARABA DA ZUWANKA YAA MAI SHIRTARWA A BAYAN MANZON ALLAH (S.A.W.W)
Ibn Jarir Addabari yace, Ahmad Bn Yahya Assufiy ya bani labari, Hassan Bn Hussaini Al-Ansaariy ya bani labari, Mu'azu Bn Muslim ya bani labari , Harwiy ya bamu labari daga Ada'i Bn Sa'ibi, daga Sa'id Bn Jubair, daga Ibn Abbas (R.A)yace, yayin da aka saukar da;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ ABIN SANI KAWAI NI MAI GARGADI NE, KUMA GA KOWACCE AL'UMMA AKWAI MAI SHIRYAR DA ITA .‘’
Sai Manzon Allah (S.A.W.W)ya dora hannunsa zuwa kafadar Aliyu yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ KAINE MAI SHIRYARWA YAA ALIYU, KUMA DA KAI NE DUKKAN MAI SHIRYUWA ZAI SHIRYU A BAYANA .‘’
MADUBI
- Tafsirul 'Dabari, J:13, SH:108.
- Mustadrak na Hakeem Annaisaburi, J:3, SH:129.
- Mujma'us-Sageer, J:1, SH:162.
- Kadibul-Baghdadi, J:12, SH:372.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~8th March, 2020.
Tags:
Munasabobi