Mafiita: Hanya Mafi Sauƙi Idan Da Gaske Ne Gwamnati Nason Kawo Karshen Annobar Coronavirus


Daga Ma'asumah Nigerian News Update.

Mai zai hana gwamnati tayi koyi da matakan da wasu Kashashe ke dauka don magance wanann annobar ta Coronavirus, koda a matakin rigakafi ne ? Munga yadda wasu kashashe su dukufa wajan dakile yaduwar wannan annoba ga yan kasarsu ta hanya mabambamta. Misali munga yadda jami'an lafiya na kasar Ghana suke bi dukkanin lunguna da sako na kasar suna yin feshin maganin hana yaduwar wannan annoba.

Amma a tamu kasar babu wani kwakwkwaran mataki da muga gwamnati ta dauka domin kawo karshen wannan annoba, face takurawa al’umma da sunan daukar mataki. Tabbas killace kai daga barin cudanya cikin al'umma itama hanyace ta yaki da wannan annoba, kamar yadda masana suka bada shawara, amma daga cikin abu mai muhimmanci akwai samar da wasu sabbin salo na yaki da cutar kamar yadda na bada misali da wasu kashashen. Da wannan al'umma zasu kara fahimtar cewa lallai gwamnati da gaske take.

Idan dai ya kasance iyakan matakin da gwamnatin Najeriya zata dauka wajan dakile wannan annoba shine hana zirga-zirga, kasuwanci, ibada a cikin jama'a da makamantansu kawai, ba tare da bullo da wasu sabbin salon yakar cutar ba, to lallai hakan zai sa a zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula ga yan kasa. Sannan zamuce manufar gwamnati shine takurawa al'umma da hanasu ibada da sunan yaki da annobar Coronavirus, domin ba a dauki matakan dasu dace a dauka ba.

Sannan ya kamata zunzurutun makudan kudaden da aka ware domin yaki da wannan cuta muga ta hanyar da ake kashesu a zahiri domin yaki da cutar. Hakan zai kara wa al'umma natsuwar cewa lallai gwamnati da gaske take, sannan kuma tana kishin al'ummarta. Idan kuwa ba haka ba, to lallai zamu zarge ta da fakewa da Coronavirus wajan cutar da al'umma.

- Abbakar Ibraheem Kudan.
  28/03/2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post