MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
________________
__abbagano ______________
Alkur'ani ya bamu
ma'aunin gane mutum
mai cikakken addini , ko
mace ne ko namiji.
saboda haka babu
bukatar mu karbi
ma'aunin Jinsi ko
bangaranci wanda
hadisai suke kokarin
nuna mana.
Tun farko Allah ya rushe
asasin cewa wai maza
sunfi mata cika da
kamalar addini, ya nuna
mana duk daya suke a
wurinsa, saidai wanda
yafi wani tsoron Allah.
1-
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻧﺎ ﺧﻠﻘﻨﺎﻛﻢ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ
ﻭﺃﻧﺜﻰ ﻭﺟﻌﻠﻨﺎﻛﻢ ﺷﻌﻮﺑﺎ ﻭﻗﺒﺎﺋﻞ
ﻟﺘﻌﺎﺭﻓﻮﺍ ﺇﻥ ﺃﻛﺮﻣﻜﻢ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ
ﺃﺗﻘﺎﻛﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻢ ﺧﺒﻴﺮ
( 13 ) ﺍﻟﺤﺠﺮﺍﺕ
Kaga a wannan ayar
karara Allah ya daidaita
mace da namiji, sannan
ya nuna takawa itace
ma'aunin fifiko a
tsakaninsu a wurin
Allah.Amma abun
mamaki sai naga wasu
na kokarin cewa wai
mata dukkansu sunada
nakasun addini, kaga
kenan bazaka hadasu
da maza ba, alhali
abunda alkur'ani ya
nuna mana ya sabama
wannan.
2-
ﻓﺎﺳﺘﺠﺎﺏ ﻟﻬﻢ ﺭﺑﻬﻢ ﺃﻧﻲ ﻻ
ﺃﺿﻴﻊ ﻋﻤﻞ ﻋﺎﻣﻞ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ
ﺃﻭ ﺃﻧﺜﻰ ﺑﻌﻀﻜﻢ ﻣﻦ ﺑﻌﺾ
Ma'auni na biyu wanda
alkur'ani ya bamu shine,
aiki, Domin Allah yayi
alkawarin cewa bazai
lalata aikin mai aiki a
cikinmu ba, namiji ne ko
mace.
Allah yana fada mana
wannan, mai cewa
ma'aunin shine JINSI
ina ya samo nashi a
alkur'ani??
3-
ﻭﻣﻦ ﻳﻌﻤﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺎﺕ ﻣﻦ
ﺫﻛﺮ ﺃﻭ ﺃﻧﺜﻰ ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ ﻓﺄﻭﻟﺌﻚ
ﻳﺪﺧﻠﻮﻥ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻭﻻ ﻳﻈﻠﻤﻮﻥ ﻧﻘﻴﺮﺍ
( 124 ) ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
Ma'auni na ukku shine
aikin kirki, Allah ya nuna
namiji ko mace duk
wanda yayi aikin kirki to
mumini ne, kuma zai
shiga aljanna baza'a
zalunceshi ko kadan ba.
To Allah ya nuna cikar
imani (wanda shine
cikar addini) yana cikin
Aikin kirki, wasu kuma
suna cewa wai saiga
namiji, domin ita mace
tanada nakasu a
addininta.
4-
ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺤﺎ ﻣﻦ ﺫﻛﺮ ﺃﻭ ﺃﻧﺜﻰ
ﻭﻫﻮ ﻣﺆﻣﻦ ﻓﻠﻨﺤﻴﻴﻨﻪ ﺣﻴﺎﺓ ﻃﻴﺒﺔ
ﻭﻟﻨﺠﺰﻳﻨﻬﻢ ﺃﺟﺮﻫﻢ ﺑﺄﺣﺴﻦ ﻣﺎ
ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻤﻠﻮﻥ
( 97 ) ﺍﻟﻨﺤﻞ
Aya ta hudu itama tana
magana akan aikin kirki
ne.
BILLAHI ALAIKUM !!!
Dukkan ayar danabi a
alkur'ani tana magana
ne akan mumini namiji
ko mace, zasu iya kaiwa
cikakken imaninsu,
amma wai an kawo
wasu ruwayoyi suna
cewa wai ma'aunin
shine: idan mace ce to
tanada nakasu a
addininta.
Miyasa zamu ajiye
Alkur:ani mu dauki
ma'aunan da zai iya
yiwuwa jinginawa
Annabi akai??.
Allah ya kyauta.
mamman amadu
ReplyDelete