Ahlulbaiti jirgin tsira



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Da sunan Allah mai murkushe azzalumai tsira da aminci su tabbata ga annabi Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka yarda da karamar ka ka kara jaddada su ga sahabbansa nagartattu.

Hakika wannan Rubutu da muka saka wa suna jirgin tsira wani huɓɓasa ne da muke kokarin yi domin isar da sakon Manzon Allah wato annabi Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka waɗanda sune suke shiryatar da mutane izuwa ga samun hasken bautar Allah sannan wannan wani kokari ne muka domin kawo maku wasu daga cikin hadisai annabi da iyalansa ma'ajiyar sirrin Allah da suka yi magana akan fannuka da dama wanda suka shafi duniyar mu da lahirar mu.

Hadisi na 1 akan hani ga rowa

Manzon Allah (s) ya faɗa cewa"Ba zai shiga aljanna ba duk wanda ya kasance marowaci, kuma rowa itaciya acikin wuta, rassanta kuwa suna  a duniya, wanda duk ya rike wani reshe daga gareta to wannan reshen zai kaishi wuta, kuma marowaci abun fushi a sammai da kasa".

Hadisi na 2 a cikin falalar kyauta

Manzon Allah (S) yace"mai kyauta abun sone a sama sannan abun sone a kasa, Kaga kyauta wata itaciya ce a cikin aljanna, rassanta suna à cikin duniya, wanda ya rataya da wani reshe daga wannan itaciya zai kaishi a aljanna, kuma kyauta itace kamalar mumini".

Hadisi na 3 a cikin hani aka ha'inci

Manzon Allah (S) yana fada cewa"Ba ya tare dani duk wanda ya ha'inci dan uwa sa a cikin iyalan sa da kuma dukiyarsa, baya tare dani wanda duk ya hana amana, kada ka hana amana ga wanda ya hana naka. Sannan Manzon Allah (S) yace"wanda duk ya hana amana a duniya sannan ba mayar da ita ba ga Ma'abotan ta ba, sannan har mutuwa tazo masa to ya mutu akan addinin da ba nawa ba, kuma zai haɗu da Allah yana fushi dashi".

Hadisi na 4 akan akan falalar kiyaye amana".

Manzon Allah (S) yace"Babu imani ga wanda bashi da amana. Kuma amana tana sauko da arziki kuma cin amana tana sauko da talauci. Ku bada amana ga waɗanda suka Baku ita".

Hadisi na 5 a cikin hani aka saɓa alkawari.

Manzon Allah (S) yace"Babu addini ga wanda bashi da alkawari. Wanda duk yayi mu'amula da muta to kada ya zalunce su, sannan ya magana dasu bai masu karya ba, sannan yayi alkawari dasu ba saɓa masu ba, to hakika yana daga cikin waɗanda muruwarsu ta chika".

Hadisi na 6 dangane da falalar cka alkawari.

Manzon Allah (S) yace"Na umurceku da Gaskiyar zance, da kuma chika alkawari, da kiyaye amana, domin wannan shine wasiyyar annabawan Allah ".

Daga karshe muna tawassuli da tsarkakan sunayenka Allah ka gaggauta kubutar da maulanmu sayyid zakzaky (H) da matarsa malama zeenatu Ibrahim da sauran yan uwa gaba daya sannan Allah ka rusa kafurci da zalunci wannan duniyar sannan ka biya bukatan dukkanin muminai maza da mata na alkhairi gaba ɗaya a duniya da lahira sannan ka karesu daga dukkan abun da suke jin tsoro sa ka kubutar musulmi daga kangin da suke ciki na zalunci.

Wassalam daga ɗan uwanku mai yawan saɓon Allah wanda yake baran addu'a daga bakunanku masu albarka.

Daga Wakilinmu
Abubakar Labbo

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post