MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Abbagano ✍️
Kadan akace( revolution) (الثور) wasu suna ganin cewa, kaman abin ya rataya da rugujewar wata gwamnati ne da kafa sabuwar gwamnati shine sauyi.
Alhali kuma abin ba haka bane,
sauyi yana nufin sauyawar tinanin al'umma da fikirarsu, misali ace ga wata alama tana rayuwa ƙaraƙashin zalumci kuma ta yadda da hakan sannan tana biyayya ga azzaluman shugabannin nan,
to idan ana buƙatar sauyi ba kawai za'a ruguje gwamnatin bane, a a akwai buƙatar samar da wasu adilai waɗanda zasu maye gurbin wannan azzaluman,
sannan su kansu al'umma akwai buƙatar afahimtar dasu cewa yanzu adalci ne yakamata su rayu akanshi sannan kuma asanar dasu maye adalci su fahimceshi da anfaninsa arayuwarsu.
To idan al'umma suka fahimci yadda yakamata su rayu to da kansu zasu iya samar da canji,
Wato tunani ake buƙatar canzawa bawai kawai gwamnatiba, domin idan an canza gwamnati amma tinanin al'umma bai canzaba to zaizama canjin ba zai haifar da natija mai kyauba.
Kuma wannan canjin al'ummar ita zata samar dashi ba daga sama za'azo acanza musuba, domin Allah (t) yana cewa;(tabbas Allah ba zai canzawa wata al'umma ba har sai suncanza da kansu)
ۗ إِنَّ اللَّـهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا بِأَنفُسِهِمْ ۗ ﴿١١﴾
سورة الرعد ، صفحة 250
To kaga kenan al'umma su zasu samar da canji, to amma ta yaya? To dole akwai abubuwa guda uku waɗanda sai sun samu sannan canji zai bada natija mai kyau.
1-shugaba.
2-hadafi.
3-mataimaka
👉1:-shugaba: dole asamu shuguba wanda zai zama shi aikinsa shine wayarwa al'umma kai, da kuma ƙiransu zuwa ga wani hadafi ayyananne wanda zai zama da fahimtar wannnan hadafinne al'umma zasu ƙauracewa zalumci, yazama basa son cigaba da rayuwa aƙarƙashin azalumci, wannan shugaban awannan nahiyar tamu shine Allama sheikh ibrahim zakzaky.
👉2:- Hadafi: Dole yazama akwai hadafi ayyananne, to ananne matsalar take idan yazama hadafi ba mai kyau bane to natijan ba zata zama mai kyauba, to amma idan hadafi yazama mai kyaune to natija zata zama maikyau, ko kuma inyazama bama hadafin, to zai zama bama natija.
👉3:- dole ne asamu mataimaka wadanda zasu dafawa jagora, wajen isar da hadafi.
Tags:
Muhimman zantuka