@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TAIMAKAWA MATA SAUKE HAQQI NE
Ban ma san da me yayi kamata ba, jahilci zan kira shi ko kuma girman kai ?
An wayi gari da dama cikin mazajen da ke taimakawa matansu wajen renon 'ya'yayensu ana fassara su a matsayin lalacewa ko kuma dai wadanda matan nasu suka fi qarfinsu.
Irin wannan fahinta ko tunani na sanya da maza dama nisantar taimakawa matansu wajen renon 'ya'yansu yayin da ayyuka suka yi musu yawa.
Abinda suka manta ko kuma suka jahilta shine, renon 'ya'ya haqqi ne da ke kan iyaye maza , mata kawai na renonsu ne a matsayin taimako wanda za ta sami lada cikinsa.
‘’ KUYI TAIMAKEKENIYA AKAN AIKIN ALKHAIRI DA KUMA TSORON ALLAH, KUMA KADA KUYI TAIMAKEKENIYA SABO (committing sin)DA KUMA ZALUNCI .‘’
(QUR'AN)
Da ace mace za ta haihu sannan tace ita ba za ta shayar da yaron ba sai an biya ta, to, babu wani zargi a kanta. Dole ne uba ya biya ko kuma ya nemi mai shayar da wannan yaro ayi ciniki.
Duk abinda mace tayi taimakonka ne, kenan idan kayi irin wannan aiki da take yi domin kai tausayawa ce ko kyautatawa.
Amma sai kaga wasu mazan na ganin daukar yaro don baiwa mata damar yin wani aiki cikin sauqi a matsayin lalacewa ko kuma tsoro.
Shi kuwa wannan bawan Allah da kuke ganinsa a hoto bai dauki yin hakan a matsayin lalacewa ko tsoron matarsa ba.
Ya kanyi hakan sau da yawa, kuma ya fito cikin jama'a da yaro goye a bayansa. Kuma shi yana ganin hakan a matsayin taimakawa matar tasa ce.
Da fatan za ku sauke girman kai maza ku sauqaqawa matanku yayin da ayyukan cikin gida yayi musu yawa.
Sannan yin hakan zai qara danqon soyayya tsakanin ku.
An riwaito cikin Sahihul Bukhari ma cewa wai Annabi (S.A.W.W)na daukar matarsa a wuya (Ummul-mumina A'isha)zuwa kallon wasa.
To, ina kuma ga kai akan 'ya'yanka?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~23rd March, 2020.