Labari Mai Dadin Ji Daga Kasar Iraki.

                       Alhamdulillah

Wasu daga cikin Almajiran Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da suke Karatu a Karbala  Al-Muqaddasa a Makarantar  Ma'ahad Warisul Anbiyya, Sun samu Sanya Rawani a hannun daya daga Malaman  Haramin Imam Hussain(As) Wato Shaikh Fahimi Al Haidari .



Cikin Farin ciki aka gabatar da sanya musu  Rawanin tare da tayasu murna da Kuma Musu Nasiha akan Wajiban da suka hau kansa bisa wannan Nauyi daya hau kansu.

'Yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky (H) Guda Bakwai ne aka Sanya Musu Rawani a Yau Litinin 16/3/2020.

Muna alfahari da ku. Allah Ya yawaita mana ire-irenku cikin almajiran Sayyid Zakzaky (H)

Ga wasu daga Cikin Hotunan









Auwal Yusuf Muhammad
#16/3/2020

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post