Iyalan tsohon shugaban hukumar kayyade farashin man fetur ta Najeriya, PPMC, Engineer Suleiman Achimugu sun tabbatar da cewa mahaifinsu ne ya rasu sakamakon annobar coronavirus.
Daga --Idishia Jos
Da safiyar Litinin din jiya ne dai hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar da rasuwar daya daga cikin mutane 35 din da ke fama da cutar ta coronavirus.
Mutuwar Engineer Sulaiman Achimugu ce dai rashi na farko da aka samu a Najeriya tun bayan shigar annobar coronavirus cikin kasar.
Duk da cewa hukumar ba ta kama sunan marigayin ba, iyalansa sun fitar da sanarwa inda suka ce ya rasu ne sakamakon annobar coronavirus.
Sanarwar wadda daya daga cikin 'ya'yan marigayin, Abubakar Achimugu ya fitar ta ce, "mahaifinmu ya rasu ranar 22/03/2020 'yan kwanaki bayan dawowarsa Najeriya daga Burtaniya, inda ya yi jinya.
Marigayin ya kwashe lokaci a wani asibiti a Burtaniyar domin jinyar ciwon daji inda ake yi masa gashi.
Ya kebe kansa bayan dawowar tasa daga Burtaniya, inda kuma bisa radin kansa ya kira hukumar NCDC bayan jikinsa ya tsananta da alamun cutar coronavirus."
Sanarwar ta kara da cewa an tabbatar da mahaifin nasu ya kamu da coronavirus, inda kuma ya ci gaba da karbar magani kafin rai ya yi halinsa ranar Lahadi.
Tuni dai aka yi jana'izar marigayin bisa tanadin addinin musulunci.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
Tags:
Labaran Duniya