Ko kun san kyauta mafi alkairi da ake bawa mutane???




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TANAN AKE GANE MAFIFICI CIKIN MUTANE

Dukiya da 'ya'ya sun kasance abin alfahari ko kuma abinda ake tinqaho dasu a duniya. Abubuwa ne biyu wadanda ke shiga cikin zukatan masu su, wanda ya same ya sami kaso mai girma na daga ni'imomin duniya.

Amma game da su Allah yayi magana don gargadin mutane a kansu inda yake cewa:

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE ABIN SANI DUKIYOYINKU DA 'YA'YANKU FITINA CE GARE KU.....‘’

Wannan na nuna mana ne cewa duk wanda ya same su ya hadu da fitina wacce sai ya dage sosai ya kubuta daga fitinansu.

Ita kuma mafi alkhairin kyautar da ake bawa mutane takan zama alkhairi ce gare su, domin takan basu kariya sabanin dukiya da 'ya'ya.

Ya zo cikin wani hadisi, daga Usamata Bn Shuraiku yace; Na kasance a wajen Manzon Allah (S.A.W.W)sai larabawa suka zo masa ta kowanne gurare, sai suka ce; ‘’ Yaa Manzon Allah, menene mafi alkhairin abinda aka bawa mutane ?‘’  Sai yace;

‘’ KYAWAWAN 'DABI'U .‘’

- Musnad Ahmad, J;4, SH:278.

- Usdul-Ghaaba, J:1, SH:81.

Wannan ita ce kyauta mafi girma wacce aka bawa Manzon Allah (S.A.W.W)har ya zama ya fi kowa cikin Manzanni da Annabawa (A.S).

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE HAQIQA KANA KAN (kyawawan)'DABI'U MASU GIRMA .‘’

           (QUR'AN)

Kuma ita ce dai kyautar da aka bawa A'imma (A.S)wacce ta bambanta su da sauran al'umma, sannan ita aka bawa Sayyid Zakzaky (H)wacce ta bambanta shi da sauran malaman zamaninsa.

Manzon Allah (S.A.W.W)yana cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ MAFI CIKAR IMANI (daga cikin)MUMINAI SHINE WANDA YA FI SU KYAWAWAN 'DABI'U...‘’

Daga cikin kyawawan dabi'u kuwa akwai:-

GASKIYA A MAGANA,

RIQE AMANA,

QIN ZALUNCI,

TAIMAKON WANDA AKA ZALUNTA,

KUNYA,

GIRMAMA NA GABA,

TAUSAYIN RAUNANA,

KAMUN KAI,

           D.S

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

~5th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post