MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Daga: Bin Haroun Sigau
-Yazo a ruwaya Manzon Allah (S) yake cewa; "Shu'aib yayi kuka, sabida soyayyar sa ga Allah, har saida ya makance, Allah ya dawo masa da ganin sa.
-Ya kara ci gaba da kuka, har saida ya kara makance wa, Allah ya kara dawo masa da ganin sa. Ya kara ci gaba da kuka, har saida ya kara makance wa, Allah ya dawo masa da ganin sa.
-A karo ma hudu ne Allah yayi masa wahayi, yake cewa; Ya Shu'aib har zuwa yaushe wannan zai daina faruwa daga gare ka? In wannan ya kasance daga tsoron wuta ne, na ƴanta ka daga gareta, in kuma sabida biɗar aljanna ta ne, na lamince maka.
-Sai Shu'aib yace; Ya ubangijina, mai girma da buwaya, ba ina kuka bane domin tsoron azabar wuta, ko do¹min neman aljannar ka ba. Kawai na gaza hakuri ne wajen muradi da zaƙuwar kan yaushe zan ganka.
-Sai Allah maɗaukakin sarki, yayi masa wahayi yana mai cewa; indai har hakane, to, zan sanya mai magana da yawuna Musa Bin Imran ya zam maiyi maka hidima."
Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad....