Ko Gwamnonin Arewa Su Farka Daga Bacci, Ko A Wayi Gari Ba Arewa, Inji Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnonin Arewa da lallai fa lokaci yayi da su farka daga barci, su san yadda za a kawo karshen hare-haren yan bindiga a yankin ko kuma a wayi gari wata ra na babu ma Arewan. Sanata Sani ya bayyana cewa ‘yan bindiga na cin karen su ba babbaka a yankin Arewa, kullum maimakon a samu sauki abu sai gaba-gaba yake yi.

Musulmai da ake kashewa bai zama abin tashin hankali ba saboda shugabannin su ba su sun su yi maganan da zai bata wa gwamnati rai, su ko kiristoci, a kullum suna fitowa su nuna damuwar su da rashin jin dadin su game da abinda yake faruwa na kashe-kashen mutane da ake yi.


Gaba daya gwamnonin Arewa suna tsoron su tunkari gwamnatin tarayya su gaya mata gaskiya, alhali a nan ana ta kashe mutanen su ana yin garkuwa da su. “Matsalar rashin tsaro a Arewa ya na samun mazauni ne a dalilin munafince-munafincen da shugabannin yankin ke yi na kin fadi wa gwamnati gaskiyar matsalolin da ake fama dasu. Sai a rika yi kamar komai lau.


Idan ana kashe mutanen mu, ana sace su, kuma muka fito muka yi magana, sai gwamnati da ‘yan kanzagin ta su fito suna cewa wai siyasa ce, ba gaskiya ba.

Daga -Idishia Jos

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post