@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HAQIQA AN ZARGI SAHABBAN ANNABI A GURARE DA DAMA
Shine Imam Ali(A.S)qanin Manzon Allah (S.A.W.W)kuma sirikinsa.
Shugaban masu imani mijin shugaban matan talikai Fatima (S.A), kuma baban shugabannin samarin Aljannah Imam Hassan da Imam Hussaini (A.S).
Shine wanda ba a kame-kame wajen kawo darajarsa, wanda ambaton darajarsa ke qara fito da darajar Annabi (S.A.W.W)ba tare da an naqasta darajarsa (S)ba. Ka san wasu in an kawo darajarsu sai an ci zarafin Manzon Allah (S.A.W.W).
'Dabarani da Ibn Abiy Hateem sun fitar daga Ibn Abbas (R.A)
yace, Allah bai saukar da :
‘’ YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI .....‘’ ba face Aliyu ne shugabanta kuma madaukakinta. Haqiqa an zargi Sahabban Annabi (S.A.W.W)a gurare da dama, amma ba a ambaton Aliyu sai da alkhairi .‘’
Domin ganin wannan magana, duba:
- Fadha'ilus-Sahaba na Ahmad Bn Hambal, SH:189.
- Zakhaa'irul-Uqba, na Muhibbuddeen 'Dabari, SH:89.
- Nurul-Absar na Shibalanji, SH:131.
Wannan shaida tana tabbatar mana ne cewa Imam Ali (A.S)ya kasance na dabam (special)ne daga cikin Sahabbai kamar yadda Annabi (S.A.W.W)ya kasance na dabam cikin dukkan Annabawa da Mursalai (A.S).
Shine wanda ke yin hukunci da Qur'ani da hadisi ba tare da Qiyasi ba. Wanda ba a samun kuskure ko nadama cikin hukunce-hukuncensa.
Haakeem ya fitar da wani hadisi kuma ya inganta shi daga Aliyu (R.A)yace:
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ Manzon Allah (S.A.W.W)ya tura ni zuwa Yamen, sai nace: Yaa Ma'aikin Allah, ka tura ni alhali ni matashi ne don nayi hukunci a tsakaninsu, kuma ban san menene hukunci ba. Sai ya bigi qirjina yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YAA ALLAH KA SHIRYAR DA ZUCIYARSA , KUMA KA TABBATAR DA HARSHENSA .‘’
Na rantse da wanda ya qagi qwaya (corn), ban taba yin kokwanto cikin yin hukunci tsakanin mutum biyu ba!‘’
(NURUL-ABSAAR NA SHIBALANJI, SH:128).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~3rd March, 2020.
F R E E
S
A
Y
Y
I
D
Z A K Z A K Y (H)!
Tags:
Taskar ilimi