Shafin dake kawo muku, dadadan labarun gida da waje cikin harshen Hausa
Daga: –Bin Haroun Sigau
Wani dan majalisar wakilai, Shehu Koko yayi kira ga shugaba Buhari a kan ya daukewa jama'a kudin wuta da na ruwa na watanni biyu
Dan majalisar wakilan na tarayya ya bayyana cewa hakan zai matukar zama tallafi ga jama'a a wannan lokacin tsananin da 'yan kasa ke ciki
Dan majalisar mai wakiltar Maiyama/Koko/Besse a tarayya ya ce duk da wadannan ababen more rayuwar ba na gwamnati bane, zai fi kyau idan aka daukewa 'yan kasa
Wani dan majalisar wakilai, Shehu Koko, yayi kira ga shugaba Buhari a kan ya bada umarnin dakatar da karban kudin wuta da na ruwa daga 'yan Najeriya na watanni biyu a matsayin hanyar sassauci garesu, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Koko mai wakiltar mazabar Maiyama/Koko/ Besse a tarayya karkashin jam'iyyar APC yayi kiran ne a takardar da ya saki a ranar Litinin.
KU KARANTA: Shekaru huɗu, wane hali Jagora yake ciki??
Wani bangaren tarkardar yace, "A halin yanzu kasar mu na cikin jarabawa kamar yadda sauran kasashen duniya suke ciki. A yayin da muke ci gaba da addu'a ga Ubangiji, ina kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da ababen more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da ruwan sha a kyauta.
"Na yarda hakan zai matukar taimako ga jama'a wajen sassauci a kan annobar da ta barke. Duk da wadannan ababen more rayuwar nan ba na gwamnati bane, muna kira ga gwamnati da ta taimaka don sassautawa jama'a,"
Tags:
Labaran Duniya