Jinsin mutane uku da ya kamata ka kasance tare da su!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ZA KA RABAUTA IN KA KASANCE TARE DA SU

Ita rayuwar duniya koyon zama ake yi cikinta, idan ka koya za ka zauna lafiya ka kuma rabauta daga gare ta.

Dole ne kasan irin mutanen da za ka zauna dasu don kyautata rayuwarka ta duniya da lahira. Duk mutanen da za ka zauna tare da su wadanda ba za qaru dasu cikin addininka ba, to, babu akhairi cikin zamantakewarku tare.

Manzon Allah (S.A.W.W)ya nusar damu game da wadanda ya kamata mu kasance tare dasu a rayuwarmu.

Ga maganar tasa nan kamar haka;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KA TAMBAYI MALUMA (kafin aikata komai naka), KA RIQA MU'AMALA TARE DA MASU HIKIMA, KUMA KA ZAUNA TARE DA FAQIRAI .‘’

(Tuhfatul-Uquul,SH: 34)

        NUSAIWA

Idan aka ce maluma ana nufin masu yin koyi ne da koyaraar Manzon Allah(S.A.W.W)ba wai masu karatu wanda ayyukansu ya sabawa abinda suka karanta ba, kuma ba masu sanyawa mutane gubar qiyayyar Annabi da iyalan gidansa (A.S)ba.

          DARASI

(1)- Idan kana tambayar maluma (yin karatu a gabansu), to, ba za halaka cikin rayuwarka ba, sannan babu nadama cikin ayyukanka.

(2)- Yin mu'amala tare da masu hikima na qarawa mutum fasaha da kuma iya zama da jama'a.

(3)- Zama cikin talakawa kan sa mutum ya zama madaukaki, domin sune za su riqa qaruwa daga gare shi ta hanyar samun taimakonsa, kuma hakan zai cire masa girman kai cikim zuciyarsa.

Yakan sa mutane suyi saurin fahintarka fiye da wanda ke nisantarsu cikin zamantakewa.

Rayuwar Annabi (S.A.W.W)kadai ta zama babban abin misali kuma abin koyi, domin dukkan rayuwarsa cikin talakawa ya yi ta. Hakan ya taimaka ta wajen amfanuwarsu daga gare shi, ba wai shi ya amfana daga gare ba.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-09039791509

~7th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post