JAWABIN SHEIK YAQUB YAHAYA KATSINA KAN CORONA VIRUS.

 Bisimillahir-rahamanirrahim
Allahumma salli ala muhammad walihi addayibina dahirin.

Da farko dai kiran mu ga al'umma baki daya bama ga wai 'yan uwa da muke wannan harka ta gwagawarmaya tare dasu ba, baki daya shine cewa mutane ya kamata su fahimci cewa wannan al'amari daga ALLAH ne kuma wani horo da punishment  daga Allah saboda gaskiyar magana anyi nisa da Allah, an bar Allah.

Alamomine na fushin Allah ga Al'ummar Duniya baki daya hatta kau koda kamar yadda ake cewa wata qasa ce ake zargi da cewa ko ita ta qirqiro wannan cuta don ta huce takaicin ta akan wasu qasashe, koda haka nanne za muga cewa kaikayine ya koma kan masheqiya.

 Dan adam ne yayi mummunan aiki ya dawo masa, ya kamata mutane su dawo cikin hayyacin su, su gane cewa sunyi nisa da Allah, ba kawai anyi nisa da Allah ta wurin bauta masa da wurin bin umarnin da hanin sa ba,
 A'a ana ma fada da Allah ne.

Duk inda kaga an daga tutar addinin akace ana kira zuwa ga Allah za kaga sun dira ana fada shi kuma Allah mai hakuri  ne, randa kuma yayi fushi ba akanji da dadi ba.

Munan aqasar da muke ciki babban misaline  malam ibrahim zakzaky (h) wanda yake malamine sannan ne mai son zama lafiya wanda yake da alaqa da kowa bama musulmi ba hadda wadanda ba musulmi ba, da kuma kokarin dora mutane kan dai dai da nuna masu abinda ya kamata.

 Dubi irin zaluncin da cin zarafin da akayi masa da kuma tsarewar da ake masa na rashin adalci wanda duniya Naji na gani tayi shiru kuma da sunan wadanda duk suke wannan aikin daga mai cewa shi krista ne sai wanda ke cewa shi musulmi ne,
Kusan duk duniya haka take tafiya daga musulmi sai krista ke juya duniyar nan, amma kuma sunayin sabanin abinda addinin ya koyar dasu.

saboda haka in Allah yayi fushi ya sanyo wani abu mai kama da irin wannan to ba mamaki, kadanne daga cikin alamomin fushin Allah ga Al'ummar duniya a yanzu.

 Banda sabo iri-iri da akeyi irinsu auren jinsi da wadatuwar maza da maza da kuma mata da mata da duk wasu abubuwa da sukayi kama da wadannan, da fandarema Allah da fada dashi da sauransu.

 Saboda haka ya kamata mutane su dawo cikin hayyacin su, su shiga taitayinsu.

Yanzu dai kiran da zamuyi ga al'umma da 'yan uwa baki daya dama kowa da kowa shine mu koma wurin Allah madaukakin sarki mune mi gafara kuma mu daina aikata abubuwan da muke aikatawa sannan kuma mu daina zalunci,

 Mahukunta masu jagorantar mutane suna zaluntar su ayi masu bayani, a gaya masu gaskiya suyi adalci, suyi abinda ya kamata, koda dokokin da suka rubuta da kansu sukace sune dokokin da suka yarda dasu bana Allah ba,  to ko su subi su idan sunbi wadannan dokokin mutane zasu zauna lafiya,
 za'a samu yadda ake buqata.

Amma ba zaiyu ya zama ba abin dokar Allah ba kuma dokar da mutane suka yarda suka yima kansu kuma ba abi sannan kuma ace za'a samu yadda akeso,

 Saboda haka kar acire hannun Allah aciki, ace dalili kaza ne, sannan abi shawarwarin likitoci duk shawarwarin da likitocin suka bada da masana akan wannan fanni na kiwon lafiya, to abi wadannan shawarwarin kuma a tsare su, sannan kuma ayi kokari ya zamana kowa addininsa kirista ko musulmi ne toya koma wurin Allah ya nemi gafara ya kuma yi addu'a Allah yaye ma duniya wannan bala'i daya tun karo ta wanda kuma ba'asan ina aka dosa ba.

 Muna fatan Allah ya kawo sauqi da rangwame ga al'umma.

Written by: Bashir Adamu mb

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post