Waki'a yanzu haka a Abuja. Yan Uwa Addu'oinku Nada muhimmanci.
Daga --Idishia Jos.
Rahoton yanzu dai mutum 2 suka Harba, sun kama yan uwa da daman Gaske sun tafi dasu. Amma dai babu Shahidi sai dai ko nan gaba, zuwa yanzu an watse.
Da misalin karfe 12 na rana daidai jirgin Muzahara #FreeZakzaky ya tashi a Layin Human Rights dake Abuja inda daruruwa matsa ke taka kwalta cikin izza da nutsuwa ana kiran gwamnati da ta gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da gaggawa, sai ga jama'an tsaro cikin mummunan shiri suna zuwa suka fara ruwa wuta cikin masu muzahara inda cikin ikon Allah sai da muzahara ta ratsa cikin su.
Zuwa yanzu ba'a tantance ko mutane nawa suka harba ba, sannan ba'a tantance mutane nawa suka kama ba. Ga wasu daga cikin Hotunan Muzaharar lumanan asaki Zakzaky kafin Jami'an Tsaro su afka musu.
#FreeZakzaky
Yahya Muhammad Soje shine ya nakalto mana wannan rohoto
Tags:
Labaran Duniya