@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BA IZALA CE LAIFI BA SAI DAI IZALANCI
IZALA:- Suna ne tamkar sunan da za ka radawa danka, ba zai taba zama muni ba matuqar ba ma'anarsa ta sabawa muslimci. Saboda haka idan aka nazarci cikakken sunan nata za muga babu aibu ko kadan cikinta.
IZALANCI:- Aqida ce wacce wanda ya ansa sunan sama IZALA ya zama tsarkakekke wanda ko ya aikata laifi ba a dubawa.
IZALA:- Akwai ta da qoqarin yawan wa'azi ga al'umma fiye da kowanne bangare don kiyaye martabar wannan suna nata.
IZALANCI:- Yin fariya da wannan aiki nasu , domin su kanga aikinsu ne ke sa abar aikata wasu ayyukan, musamman ma dai bidi'a.
IZALA:- Suna da kiyaye lokaci cikin lokutan da suka tsara don gudanar da wani programme nasu, wajen farawa da kuma tashi.
IZALANCI:- Hanyar da suke bi wajen isar da saqo babu hikima cikinta, domin furucinsu yakan nisantar da jama'a daga fahintarsu.
IZALA:- Suna da qoqarin neman ilimi sosai, musamman ma na alqur'ani wanda ya fi kowanne karatu samun lada.
IZALANCI:- Son shugabanci/jagoranci a duk inda suka sami kansu, alhali son shugabanci fitina ce.
◉Taqaitacen tarihin Abul Fadalul Abbas
IZALA:- Suna da sha'awa da son ma'abocin addini, da fatan ya kasance cikin tafiyarsu.
IZALANCI:- Duk karatun mutum da kiyaye miyagun ayyukan da Allah ya hana, matuqar ba Izala yake yi ba ba sa daukarsa cikakken musulmi.
NB:- Duk abubuwan dana kawo qarqashin IZALANCI, ba ina nufin dukkan 'ya'yan IZALA ne ke da wannan IZALANCIN ba.
Saboda haka akwai masu yin IZALA amma ba IZALANCI ba, sai dai kadan ne daga cikinsu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~30th March, 2020.
Tags:
Muhimman zantuka