Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da samun nasarar warkar da mutane kusan dubu shida da suka kamu da cutar nan ta coronavirus tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.
(Rhoton abna24.com) Mataimakin ministan lafiya na ƙasar ta Iran Mr. Ra’isi ne ya sanar da hakan a yayin da yake ƙarin bayani dangane yanayin yaɗuwar cutar da kuma irin matakan da ake ɗauka wajen faɗa da ita inda ya ce ya zuwa yanzu dai an samu nasarar warkar da mutane 5710 cikin mutane 17,361 da suka kamu da cutar a duk faɗin ƙasar
Mataimakin ministan ya ce ya zuwa jiya ɗin dai adadin mutanen da suka kamu da cutar a duk faɗin Iran shi ne mutane 17,361 sannan adadin waɗanda kuma suka rasa rayukansu sun kai mutane 1135.
Jami’an ƙasar ta Iran dai suna ci gaba da kiran al’ummar ƙasar da su ci gaba da zama a gidajensu da kuma nesantar duk wani taro na jama’a a ƙoƙarin da ake yi na guje wa yaɗuwar cutar.
Tags:
Labaran Duniya