Wannan wani irin rashin imani ne, Nan gawarwakin Mutanen da wasu 'Yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ne, 'Yan bindigar sun shiga garin sun kashe a kalla mutane sama da 50+, Sun 'kona gidajen Mutane, sun dauki lokaci me tsawo suna ta'addanci a garin, Amma Gwamnan Jihar Kaduna Elrufa'i bai tura jami'an tsaro sun kare rayukan Al'ummar garin ba, Har suka gama ta'addancin su suka tafi, Babu wani daukin gaggawa daga gwamnati, Don haka ba'a kama koda mutum daya daga cikin 'Yan Ta'addan ba.
Duk da cewa gwamnan jihar kaduna Elrufa'i ya shahara wurin nuna karfin iko da mulki yana tura jami'an tsaro suna kashe 'Yan Uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky a fadin jihar, Amma sai gashi elrufa'i ya kasa nuna karfi akan 'Yan Bindiga da masu satar Mutane a fadin jahar, Amma yana nuna karfi akan raunanan 'Yan Shi'a saboda yaga su basa dauke da makami.
Allah ya jikan wayanda suka Mutu.
Ku kasance da Ma'asumah Nigerian News Update Dan kawo muku ingantattun Labarai.
Tags:
Labaran Duniya