Imani a wannan zamani, ya fi na zamanin Annabi (s.a.w.w) bada mamaki!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KARANTA KAFIN KA ZARTAR DA HUKUNCI

Bai zama abin mamaki ba ya zama masu imani a wannan zamani sufi wasu daga cikin masu imani a zamanin Manzon Allah (S.A.W.W).

Imani a zamanin Annabi (S.A.W.W)ya kasu kashi-kashi, akwai wanda ya gaskata Manzo bisa abinda yazo da shi , saboda haka za ka same shi cikin biyayya ga dukkan umarni ko hanin Manzon Allah (S.A.W.W), ko da kuwa abin ya saba son ransa.

Sannan akwai wadanda suka sallama al'amarinsu gare shi bisa tilas don tseratar da rayukansu da dukiyarsu. Su irin wadannan mutane sune suka riqa bawa Manzon Allah zafin kai da kuma yin tawaye ga umarninsa (S.A.W.W).

Su kuma na wannan zamani, duk wanda kaga ya yi imani da Allah da Manzonsa, to, za ka tarar imani ne bisa yaqini ba bisa tilasci ba, sai dai kuma hakan bai hana wasunsu sabawa Manzon ba cikin umarni da hani nasa.

Wata rana Manzon Allah (S.A.W.W)na cikin sahabbansa sai yake tambayarsu cewa:

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ WADANNE MUTANE NE IMANINSU YA FI BA KU MAMAKI ?‘’ Sai suka ce Mala'iku. Sai yace;

‘’ TO, SU KUMA WACCE HUJJA CE GARE SU DA BA ZA SUYI IMANI BA ALHALI SUNA WAJEN UBANGIJINSU ?Suka ce, to, Annabawa.

Sai yace; ‘’ SU KUMA WACCE HUJJA CE GARE SU DA BA ZA SUYI IMANI BA ALHALI WAHAYI NA SAUKA GARE SU?‘’ Suka ce, to, mune.

Sai yace, ‘’ WACCE HUJJA CE GARE KU DA BA ZA KUYI IMANI BA ALHALI INA NAN A TSAKANIN KU ? SAI DAI MUMINAN DA IMANINSU YAFI BADA MAMAKI SUNE JAMA'AR DA ZA SU ZO A BAYANKU, SUN SAMI LITTAFI (rubuce)KUMA SUKA YI IMANI DA ABINDA KE CIKINSA (ba tare da ji ko ganin wanda yazo da shi ba).‘’

‘’ WADANNAN SUNE MASU IMANI DA GHAIBU.‘’

(Suratul-Hadid)

- Ka duba sharhin farko cikin Bukhari, me suna KITABUL-EEMAN.

Saboda haka idan kayi imani a wannan zamani kuma ka bi umarnin Manzo (S.A.W.W)za ka iya fin wanda yayi imani a zamaninsa, sannan kuma ya saba umarninsa a bayansa.

Duba khudubar ghadeer mana ka ga inda Annabi (S.A.W.W)ke cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ WANDA KE NAN YA ISARWA WANDA BA YA NAN, DOMIN DA YAWA DAGA WADANDA AKA ISARWA SUN FI KIYAYEWA FIYE DA WADANDA SUKA JI (kai tsaye daga gare shi).

AI KUWA ABINDA YA FARU KENAN KO?

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-09039791509

~1st March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post