@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SARA 16 AKAYI MIN INJI IMAM ALI(A.S)
Cigaba:-
Bayan Annabi (S.A.W.W)ya ware mutum 50 ya zaunar dasu jikin dutsen Uhud kuma yace musu kada su kuskura su bar gurin, ko nasara ko shahada ✌🏽, amma sai suka saba umarninsa wanda hakan yayi sanadin yin nasarar a kansu.
Da farkon yaqin musulmai sun fara yin nsara suna korar arna suna dibar ganima. Ganin wannan nasara da kuma kwadayin ganima sai wannan mayaqa 50 da aka ware suka bar gurin da aka umarce su da tsayawa.
Ashe duk abinda suke yi Khalid Bn Walid na lura da su, saboda haka sai ya ja zugarsa ya zagayo ta bayan wannan dutse suka ritsa da musulmai a tsakiya. Suka kashe Abdullahi Bn Jabir shugaban wannan mayaqa 50 din da Annabi (S.A.W.W)ya ware su.
An yiwa musulmai jina-jina, domin har Annabi (S.A.W.W)ma an zubar masa da haqora a wannan yaqi, su kuma sauran musulmai suka gudu suka bar Annabi (S)da mutane 6, wato su 7 kenan gami da shi.
Ibn Ishaq yace;‘’ Nasarar Uhud ta samu ne sakamakon haqurin Aliyu .‘’
Shi kuma Hafiz Muhammad Bn Abdul-Azeez Al-Janabuziy ya kawo cikin littafinsa me suna (MU'ALIMUL-ITRATIN-NABAWIYYATI), daga Qais Bn Sa'ad, daga babansa cewa ya ji Imam Ali (A.S)na cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ Sara 16 akayi min a ranar Uhud, kuma sara 4 (daga cikinsu)kowanne sai da ya kaini qasa. Sai wani mutum mai kyakkyawar fuska mai dadin qamshi yazo ya dafa kafadata ya miqar dani, sannan yace;
‘’ KA FUSKANCE SU, DOMIN KANA KAN 'DA'AR ALLAH DA TA MANZONSA, KUMA SU MA SUNA YARDA DA KAI .‘’
Sai na jewa Manzon Allah (S.A.W.W)na ba shi labari, sai yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ LALLE ALLAH YA TABBATAR DA GANINKA, AI WANNAN JIBRIL (A.S)NE !‘’
(Nurul-Absar, shafi na 141-142)
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-09039791509
~15th March, 2020.