@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SUNYI MUSAYAR KALMOMI DA AMRU BN ABDUL-WUD
Cigaba:-
Da Amru yaga Imam Ali(A.S)ya fito,sai ya soma rera waqa kamar haka:-
Haqiqa na himmatu ina kira;
Ga jam'inku shin akwai mai tarya ta;
Na tsaya yayin da jarumai suka tsaya;
Irin tsayuwar qaho wanda ba ya gushewa;
Ni kuma ban gushe ba;
Ina barranta kafin tsanani;
Sai ga wani jarumi daga matasa;
Ya fito daga mafi khairin masu garari.
Sai Imam Ali(A.S)ya amsa masa kamar haka:-
KADA KAYI GAGGAWA GA NI NAN TAFE;
INA MAI AMSA KIRANKA BA TARE DA GAZAWA BA;
MA'ABOCIN NIYYA DA BASIRA;
DA GASKIYA MAI TSERATAR DA DUKKAN MAI RABO;
BUQATATA GARE KA ITA CE;
NAYI SANADIN JANA'IZARKA;
DAGA SARA WANDA AMBATONSA ZAI WANZU;
CIKIN DUKKAN FITINANNU MASU NEMAN YAQI!
Bayan wadannan baituka da Imam Ali (A.S)yayi don maida martani ga Amru, sai kuma yace;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YAA KAI AMRU, HAQIQA KA 'DAUKARWA KANKA ALQAWARI CEWA BABU WANI DAGA QURAISHAWA DA ZAI KIRAYE KA CIKIN 'DAYAN ABUBUWA BIYU FACE KA AMSA MASA 'DAYA DAGA CIKINSU !‘’
Amru yace, ‘’ Eh, hakane .‘’
Sai Imam Aliyu (A.S)yace masa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ TO, LALLE NI INA KIRANKA ZUWA GA ALLAH DA MANZONSA DA MUKA MUSLIMCI .‘’
Amru yace, ‘’ Lalle in dai wannan ne bana buqata !‘’
Sai Imam (A.S)yace masa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ TO, IDAN KA QI WANNAN, LALLE NI INA KIRANKA CEWA KA SAUKO (daga kan Doki naka).‘’
Amru yace, ‘’ A'a yaa dan dan'uwana (Oh my brother's son, I can't do this with you), ni bana so na kashe ka domin babanka masoyina ne.‘’
Sai Imam (A.S)yace masa,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ AMMA WALLAHI NI INA SO NA KASHE KA !‘’
Jin wannan furuci na Imam Ali (A.S)ya fusata Amru, sai ya diro daga kan Dokinsa.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~20th March, 2020.