@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
WALLAHI BA ZAN BARKA BA HAR SAI NA GAGGAUTA KAI KA WUTA DA TAKOBINA
Yaqin Uhud shine yaqi na biyu wanda akayi shi a tarihin muslimci wanda aka yi shi ranar Asabar 10th Shawwa, 3 (B.H).
Shi ba kamar yaqin Badr bane, domin wannan yaqi ya tsananta ga musulmai harta kai yadda aka sami Shahidai 70 da kuma munanan raunuka ga musulmai.
Dalilin wannan yaqi shine, jin zafin kisan da aka yiwa manya daga cikin jagororin kafirai Makka a yaqir Badr yasa suka yi kyakkyawan shiri don daukar fansa.
Lalle kuwa shiri yayi shiri, tanadi ya yi tanadi, domin a wannan rana sun fito cikin runduna ta mutane dubu goma (10,000), yayin da musulmi suke su dari bakwai (700)ne kacal.
Ganin haka sai Annabi (S.A.W.W)ya ware mutane 50 daga rundunarsa yace su tsaya jikin wani dutse don toshe hanyar da kafirai za su iya bi su shigo, kuma yace musu duk abinda suka ga na faruwa kar su kuskura su baro gurin.
Daga Ibn Abbas (R.A)yace, yayin da aka fito filin daga sai 'Dalha Ibn Abiy 'Dalha ya fito yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ YAA KU SAHABBAN MUHAMMAD ! KUNA RIYAWA CEWA ALLAH ZAI GAGGAUTA KAIMU WUTA DA TAKOBINKU, KUMA YA GAGGAUTA KAI KU ALJANNAH DA TAKOBINMU, TO, WAYE CIKINKU ZAI FITO YAYI MUBARAZA DA NI?‘’
Sai Imam Ali (A.S)ya fito ya tunkare shi yana cewa;
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ WALLAHI BA ZAN GYALEKA BA HAR DAI NA GAGGAUTA KAIKA WUTA FA TAKOBINA !‘’
Mutane 21 ne aka iya kashewa daga cikin kafirai a wannan,yaqi.
Abinda aka yi ittifaqi a kansa shine, Imam (A.S)kadai ya kashe mutane 7 daga cikin 21.
Daga cikin wadanda Imam ya kashe akwai:-
1- 'Dalha Bn 'Dalha,
2- Abdullahi Bn Jameel,
3- Abal-Hakaam Bn Akhnaas,
4- Sabaa'a Bn Abdul-Azeez, da
5- Abah Umayyata Bn Mugirata.
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~15th March, 2020.