Imam Ali (AS) à yakin Khandaq (5)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YA KASHE MAKASHIN JARUMAI 1000

A yayim da Amru ya dirgo daga kan Dokinsa, farkon abinda ya fara shine sare qafafun Dokin nasa don ya razanar da qananan jarumai.

Yayi ihu yayi kirari ta yadda duk Sahabban Annabi (S.A.W.W)suka ji kamar za su nutse a qasa, kuma suna ganin Imam Ali (A.S)ya kai kansa mahallaka.

Ta bangaren kafirai kuma suna ta tsalle da murnar cewa Amru zai kashe Imam Ali (A.S).

Da Amru ya tunkaro Imam Ali (AL-HAKEEM, AL-KARRAR)da nufin mubaraza da shi, sai Imam yace masa,

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ ASHE BA KA KAI JARUMI BA TUNDA BA ZA KA IYA TUNKARATA KAI KADAI BA !‘’

Jin wannan magana ta Imam sai Amru ya juya baya don yaga wa ke biyo shi a baya. Juyawarsa ke da wuya sai Imam Ali (A.S)ya sare masa qafafuwansa ya zubar da shi qasa rigijaa kamar yadda shima ya yiwa Dokinsa.

Wannan sara da Imam ya yiwa Amru yasa dukkan kafirai suka tarwatse suka juya gida da gudu.

Shine Allah(T)yake bamu labari cikin littafinsa mai tsarki;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA ALLAH YA JUYAR DA KAFIRAI CIKIN BAQIN CIKINSU (na rashin nasara), BA SU SAMI WANI ALKHAIRI BA. KUMA ALLAH YA ISARWA MUMINAI YAQI (ta hannun Aliyu). KUMA ALLAH YA KASANCE MAI QARFI (akan dukkan wani ja'iri)MABUWAYI (akan komai)!‘’

(AHZAB, AYA TA 25)

Anan ne Annabi (S.A.W.W)yace,

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ SARAN DA ALIYU YAYI A RANAR KHANDAQ YA FI ALKHAIRI FIYE DA IBADAR SAQALAINI (mutum da aljan)!‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

     09039791509

~21st March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post