@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SHI KADAI YA IYA TUNKARAR AMRU BN ABDUL-WUD
Cigaba:-
Bayan Amru Bn Abdul Wud yayi nasarar tsallakowa bangaren musulmi, abinda ya fara fitowa daga bakinsa shine,
‘’ SHIN, AKWAI WANDA ZAI TUNKARE NI ?‘’
Babu wanda yayi motsi saboda tsananin firgita da tsorata, sai Imam Ali (A.S)ya miqe zai tunkare shi, sai Annabi (S.A.W.W)yace masa kada yaje.
Amru ya cigaba da fadin cewa,
‘’ SHIN, AKWAI WANDA ZAI TUNKARE NI?INA WANNAN SOYAYYAR TAKU (ga shugaban naku)! INA ALJANNAR TAKU WACCE KUKE RIYAWA CEWA WANDA AKA KASHE (daga cikinku)ZAI SHIGE TA!! YANZU DUK CIKINKU BABU WANDA ZAI FITO YA TUNKARE NI!!!‘’
Subhanal-Lah, wallahi babu wanda ke iya yin motsi saboda tsorata, Annabi,(S.A.W.W)kuma nanan ya zura musu ido yaga ko wani zai iya fita ya tunkare shi.
Babu wanda ya fita sai Imam Ali (A.S)ya qara miqewa zuwa wajen Manzon Allah (S.A.W.W)yace masa,
‘’ ZAN TUNKARE SHI YAA MA'AIKIN ALLAH !‘’
Sai Annabi (S.A.W.W)yace,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ AMRU NE FA (yaa Aliyu).‘’
Sai Imam (A.S)ya amsa masa da cewa,
‘’ KO YA KASANCE AMRU NE (zan tunkare shi).‘’
Daga nan Manzon Allah (S.A.W.W)yayi masa izni, kuma ya cire rawanin da ke kansa (S.A.W.W)ya nada masa (A.S), sannan yace,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
‘’ JE KA AKAN SHA'ANINKA !‘’
Imam Ali (A.S)ya fito yana tafiya ta qasaita , Amru kuma ya soma rera waqa kamar haka:-
ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~19th March, 2020.