Imam Ali (As) a yaƙin Khandaq (2)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MU MIQA MUHAMMADU KAWAI MU HUTA IN JI MUNAFUKAI

Cigaba:-

Wannan rami da aka tona don ya zama kariya/shamaki ake kira KHANDAQ wanda yasa ake kiran yaqin da wannan suna kenan.

Ganin wannan dandazo na kafirai yasa munafukai ke cewa in dai za su miqa Muhammadu ga kafirai su tsira da rayukansa gara suyi haka su huta.

Su kayi ta yin gunaguni tare da zargin Annabi (S.A.W.W)wai ya jawo musu halaka. Shine Allah (T)ke bamu labari cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA A LOKACIN DA MUNAFUKAI DA WADANDA AKWAI CUTA (ta kafirci)CIKIN ZUKATANSU KE CEWA, ‘’ ALLAH DA MANZONSA BA SUYI MANA WA'ADIN KOMAI BA FACE RUDI !‘’

 (Ahzab, aya ta 12)

A daidai lokacin da munafukai ke tunanin miqa Manzon Allah (S.A.W.W)ga kafirai a kashe shi su kuma su tsira da rayukansu, su kuma muninai sun qara samun yaqini ne da kuma qara gaskata Manzon Allah (S.A.W.W) .

Shine Allah (T)ya yabe su da cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ KUMA A LOKACIN DA MUMINAI SUKA GA QUNQIYOYI (na kafirai sun tunkare su), SAI SUKA CE, ‘’ WANNAN NE ABINDA ALLAH DA MANZONSA SUKA YI MANA ALQAWARIN (zuwansa), ALLAH DA MANZONSA YA YI GASKIYA.‘’ KUMA (ganin) WANNAN (runduna ta kafirai)BA TA QARA MUSU KOMAI BA FACE (qara yin)IMANI DA SALLAMAWA (ga Allah da Manzonsa)!‘’

 (Ahzab, aya ta 22)

Wannan rami da musulmai suka tona ya taimaka musu sosai wajen hana kafirai isowa kai tsare ga musulmai.

A lokacin da kafirai suka yi nufin shiga garin Madinah don su ritsa da Annabi (S.A.W.W)a cikin gida sai suka tarar da wannan wakeken rami wanda ya hana su shiga garin Madinah.

Amma duk da haka sunyi qoqarin tsallake wannan rami don isa ga musulmi, wasu suka fada cikinsa wasu kuma suka yi nasarar tsallakewa.

Amru Bn Abdul Wud jarumi ne wanda shi kadai ke yin mubaraza da mutane dubu (1000), kuma yana daga cikin wadanda suka tsallake wannan rami cikin izzah.

Ganin Amru ya tsallako zuwa bangaren musulmi yasa wasu yin kashi cikin wandunansu.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~19th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post