Imam Ali (AS) a yaƙin Khandaq (1)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SALMANUL-FARISI YA BADA KYAKKYAWAR SHAWARI

Wannan yaqi da ya faru a Shawwal, shekara ta 5 bayan Hijra, shine ake kira da yaqin AHZAB (gangami), domin yaqi ne wanda ya tattara maqiya muslimci da suka hada da larabawan Quraishawa da kuma Yahudawan Madinah don su murqushe qaramar jama'a ta musulmi da ke zaune cikin garin Madinah.

Huyayy Ibn Akhtab shine jagoran Yahudawa Banu Nadir wanda ya kitsa wannan yaqi, kuma ya nemi hadin kan kafiran Quraishawa da wasu qabilu da suka hada da:-

Banu Ghadfan,

Banu Qayysi,

Banu Ghaylan,

Banu Qayyai,

Banu Murrata,

Banu Fazara,

Banu Sa'id,

Banu Asad,

Banu Sulayman da dai sauransu.

Suka hada qarfi don fuskantar musulmi raunana.

Banu Quraizah wadanda ke zaman lafiya da musulmai a garin Madinah, tare da alqawarin taimakon juna daga dukkan wani yaqi da za a kawo musu, sai suka saba wannan alqawari ta hanyar bawa Huyayy Ibn Akhtar goyon baya don yaqar Manzon Allah (S.A.W.W).

Sun hada gangami na mayaqa sama da mutane dubu goma (10,000)don yaqar musulmi da basu wuce 3000 ba, suka bullo musu ta kowacce kusurwa.

Tabbas, musulmai sun firgita sosai a wannan rana, shine Allah (T)ke bamu labari cikin Alqur'ani mai tsarki cewa;

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ A LOKACIN DA SUKA ZO MUKU DAGA SAMANKU DA KUMA QASA DAGA GARE KU, KUMA A LOKACIN DA IDANUWA SUKA KARKATA (saboda tsoro), KUMA ZUKATA SUKA KAI MAQOSA (kamar za su nutse qasa saboda firgita), KUMA KU KAYI TA ZACE-ZACE GA ALLAH.

A CAN AKA JARRABI MUMINAI, KUMA AKA GIRGIZASU GIRGIZAWA !‘’

  (Ahzab, aya ta 10-11)

Ganin wannan gangami ne yasa Manzon Allah (S.A.W.W)ya nemi shawarin sahabbansa kan me ya kamata su yi?

Shine Salmanul-Farisi (R.A)ya bada shawarin tona rami (KHANDAQ)da zai shiga tsakaninsu da mahara.

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~18th March, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post