MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Shafi domin kai da al'ummar ka
Daga: Abba Gano
Ubangiji subhanahu wata'ala ya karfafa magana akan hijabi ga mace, domin kiyaye mutumcinta da karamarta a cikin Al'umma, a wurare da dama a cikin Alkur'ani mai girma. Daga cikinsu akwai :
1-يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا
الأحزاب (59)
Ubangiji ya umurci annabinsa ya gayawa 'ya'yansa da matan muminai, su lullube jikinsu da hijabi.
Sannan ubangiji ya kawo hikimar hakan duk a cikin aya guda inda yace : ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ wannan shi yafi kusa kada a ganesu, ballantana a cutar dasu.
👉Zamu iya lura cewa hikimar hijabi shine, dukkan mai sanya hijabi, to ana mata kallon mace mai kamun kai, hakan zai bata kariya daga fasikai da mutanen banza da wadanda kan iya shiga mutumcinta. Domin hatta mutumin banza idan yaga mai hijabi yasan cewa wannan ba irin wadda yake aukamawa bace.
2- وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَاعًا فَاسْأَلُوهُنَّ مِن وَرَاءِ حِجَابٍ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ
A wannan ayar Ubangiji ya umurci sahabban Annabi cewa (idan zaku yambayesu wasu kaya, toku tambayesu ta bayan hijabi....)
A karshen wannan ayar Allah ya bayyana mana cewa ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ wannan shi yafi tsarki ga zuciyarku da zuciyarsu.
Kenan daga cikin hikimar hijabi akwai sanya tsarkin zuciya a cikin Al'umma. Wanda sanannen abune cewa mutane ma