Hanyoyin Da Za Ki Gyara Fatarki


Ma'asumah Nigeria News Update

M.N.N.U.030

Babu wata mace da ba ta so a ce fatarta tana sheki da yalki, babu kuma macen da take so a ce fatarta ba ta da kyau ko daukar hankali. Hakan ya sanya mata da yawa ke kashe makudan kudade wajen lura da fatar jikinsu ko ta fuska. Da yawa daga cikin mata kuma sun fada tasku sakamakon amfanin da mayukan da suke da sinadarai, wanda a maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu sai su buge da da-na-sani. Wannan dalili ya sanya shafin nan naku na ma'asumah nigeria news updates ya kawo maki hanyoyi 6 da za ki bi wajen kula da fatarki ba tare da taraddadin ko fatarki za ta gamu da wata matsala ba.

Ga hanyoyin kamar haka:-

1. Ki samu kukumba sai ki yayyanka ta, daga nan sai ki nika ta, sannan ki ajiye ta gefe guda. Hada ruwan Rose Water da ruwan lemon tsami ko jus din lemon tsami. Bayan nan sai ki hada su waje guda da kukumbar, sai gauraya sosai. Bayan kin yi haka sai ki shafa a fuskarki ko sauran fatar jikinki, sannan ki kwanta har zuwa wayewar gari. A lokacin da kika zo wankewa, sai ki samu ruwa mai dumi. Hakan zai kara wa fatarki lafiya da kuma sheki.


2. Hanya ta biyu ita ce, ki samu madarar shanu wacce ba a dafa ba, sai ki samu gishiri da kuma cokali biyu na ruwan lemon tsami ko ruwan jus din lemon tsami, sannan ki gauraya sosai. Bayan nan sai ki samu auduga ko tsumma mai tsabta sannan ki rika dongala kina gogawa a jikinki ko a fuskarki. Bayan nan, sai ki wanke jikinki ko fuskarki da ruwa mai dumi. Hakan zai cire miki dukkan dattin da ke makale a kofofin fatarki.


3. Hanya ta uku ita ce, ki gauraya ruwan Rose Water da kuma ruwan lemon tsami. Ki shafa a fuskarki ko jikinki. Yin hakan zai cire tabon da yake fata ko fuska, sannan yin hakan zai sanya fata ta yi laushi da danshi.


4. Ki samu lemon zaki sai ki yayyanka, daga nan sai ki markada. Bayan nan sai ki shafa a fuska ko a jikinki. Wannan zai sanya miki laushin fata.


5. Ki samu karas sai ki markada, daga nan sai ki shafa a fuskarki ko jikinki. Bayan awa biyu sai ki wanke da ruwa mai dumi. Yin hakan zai sanya jikinki ya rika haske da kuma daukar hankalin duk wanda ya kalle ki.


6. Ki samu kurkur sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun. Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi. Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata.

Ma'asumah Nigeria News Update.


Tare da Sakina Ahmad da Asiya A Abdussalam

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post