Hakikanin Hijabi ga mace (4)



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE


Abbagano ✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Akwai alaka tsakanin TAQAWA da HIJABI,  dukkansu sutura ne, amma Takawa suturar zuciya ne, shikuma hijabi suturar Gangar jiki ne kuma yana taimakawa wurin samu takawa da isa zuwaga Allah, idan mace bataji kunyar ubangijinta ba, bazataji kunyar fidda tsiraicinta gaban kowa ba.

Wani daga masu hikimar sahayoniyawa yana cewa : Ya zama dole mu cire hijabi daga kan mace , mu lullube alkur'ani dashi. Domin mu jefi tsutsu biyu da dutse daya , sune : ruguza mace da ruguza tsarin musulinci (isa zuwaga Allah).

Hijabi ba kawai a shari'ar musulunci aka wajabtashi ba, a'a akwaishi a dukkan addinan da sukazo daga Allah, kamar kiristanci da yahudanci dss.

Sannan hijabi bai taba hana mata taka rawa a cikin al'umma ba, a kowane fanni kuwa. Muna ganin cigaban da suka kawo. Saidai abun takaicin shine wasu matan sun maida hijabi shine wannan abunda ake lullubawa saman kai kadai. Alhalin hijabi shine riko da dukkanin sharuddansa na shari'a.  Abunda yafi ciwo shine kaga irin wannan nau'i na rashin kamun kai a gidan wasu manyan mutane a cikin al'umma wanda suke da'awar wayewa a cikin wannan zamani.

Alhalin ubangiji ya daukaka al'amarin mace, ya kimanta ta, ya 'yanta ta daga kangin jahiliyya, ya bata 'yancin rayuwa da mutumcinta , bayan ta kasance abun kunya idan  aka haiama mutum ita.

Fatan Allah ya tsarkake ruhinmu baki daya, ya bamu ikon cika sharudda

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post