Hakikanin Hijabi ga mace (3)



MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Abbagano ✍️
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Koda yake wasi suna ganin cewa hijabi shine dalilin rashin cigaban mata a duniya, sai mu tambayae shi :

Shin fitarata babu hijabi a kasashen turai ya kawo masu cigaba da kirkire kirkire kuwa a cikin al'umma ?? Koko dukkan wadanda suka shahara daga cikin mata daga mawakiya sai waddana ake tallar sabulu da hotonta ko 'yar film, shin wannN shine cigaban?

Hakika suturce tsiraici ga mace dabi'a ce ta mutumtaka, dukkan wanda suke da'awar a cire hijabi to suna fada da wata dabi'a ne daga dabi'un da Allah ya halittama mace :

: "يَا بَنِي آدَمَ قَدْ أَنزَلْنَا عَلَيْكُمْ لِبَاسًا يُوَارِي سَوْآتِكُمْ وَرِيشًا وَلِبَاسُ التَّقْوَىٰ ذَٰلِكَ خَيْرٌ ۚ ذَٰلِكَ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ لَعَلَّهُمْ يَذَّكَّرُونَ".
((YAKU 'YA'YAN ADAM, HAKIKA MUN SAUKAR MAKU DA SUTURA DA ZATA RUFE TSIRAICINKU, AMMA TUFAFIN TAQAWA SHINE MAFI ALKHAIRI, WANNAN DAGA CIKIN AYOYIN ALLAH NE KO SUN TUNATU))

Hakikanin hijabin shari'a shine wanda ya cika dukkan sharudda, amma dinka yadi bazai iya zama hijabi ba indai bai cika sharudda ba

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post